Bayan shekaru 15, Tiwita ta samar da tsarin gyara rubutu bayan wallafawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Dandalin sada zumunta na Tiwita, a ƙarshe, ya fitar da fasalin da aka daɗe ana nema na damar yin canje-canje ga rubutu bayan an wallafa, wato ‘Edit Tweet’.

Kamfanin a ranar Alhamis, 1 ga Agusta, 2022, ya bayyana cewa, wasu masu amfani za su iya fara ganin fasalin gyaran rubutun a cikin manhajarsu saboda daman an daɗe a jiran hakan.

A cewar Tuwita, fasalin a halin yanzu yana fuskantar ‘gwajin ciki’.

“Ma’aikatan ciki neza su fara amfani da sabon fasalin na ‘Edit Tweet’, sannan kuma a faɗaɗa shi zuwa ga yawan masu biyan kuɗi na ‘Twitter Blue’”, inji kamfanin.

“‘Edit Tweet’ wani fasali ne da ke ba mutane damar yin canje-canje ga rubutunsu bayan an wallafa shi,” inji kamfanin a shafinsa.

Ya ce, “Hakan zai ba da damar yin abubuwa kamar gyara rubutun, ƙara alamun da aka rasa da dai sauransu.”

A ƙarƙashin sabon fasalin, masu amfani za su iya gyara rubutunau a cikin mintuna 30 bayan su wallafa, ta hanyoyin da za su lura da canje-canje a bayyane don taimakawa kare mutuncin tattaunawarsu da gyara rikodin ɗin da suka yi da jama’a.

Tun lokacin da aka bayyana Tuwita a cikin 2006, tushen amfani da shi ya kasance mai sauqi, kuma a lokaci guda mai wahala, domin idan mutum ya rubuta abu ya wallafa, bai da damar gyarawa sai dai ya jira abin da zai biyo baya. Rubutu a manhajar ya kasance ‘baki ke yanka wuya’.

Wannan ya sa fasalin gyare-gyare na iya zama babban canji a manhajar na kafofin watsa labarun tun 2017, lokacin da Tuwita ya ƙara iyakar halin saƙonni zuwa haruffa 280 daga 140.