Jami’ar Maryam Abacha ta karrama Atiku, ta sanya wa wata tsangaya sunansa

Daga AMINU AMANAWA

A yayin wani taro mai cike da tarihi, Jam’iar Maryam Abacha American University ta Najeriya ta karrama ɗan takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP a zaɓen baɗi, Atiku Abubakar, inda ta sanya wa wata tsangaya sunansa.

Ginin tsangayar mai suna Atiku Abubakar, yana ɗauke da kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa da sha’anin Mulki, Atikun ne da kansa ya ƙaddamar da shi.

A taron ƙaddamarwar da ya sami halartar manyan mutane a Kano, wanda ya kafa jam’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jinjina wa Wazirin Adamawa, inda ya bayyana shi da wata maɓuɓɓugar ilimi da ƙarfafa gwiwa ga matasan Najeriya. Ya ce, jam’iar da Atiku ya kafa a Yola ne abinda ya sanya shi buɗe tasa jami’iar a Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar, kuma da zai buɗe abokan hulɗarsa sun tura shi wurin Atiku, domin samun shawarwari.

Sai ya gode wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar bisa yadda ya xora shi a hanya, inda ya ce, Najeriya na buƙatar mutum mai ƙwarewa kamar Atiku wanda ya sanya sha’anin ciki da wajen Najeriya, domin ci gaban ƙasa. Ya kuma buƙaci matasa su yi koyi da mutane irin Atiku da suka cimma nasarori a rayuwa.

A nasa jawabin ɗan takarar na PDP, Atiku Abubakar, ya ja hankalin hukumar jam’iar bisa wannan girmamawa. Ya kuma bada labarin yadda ya haɗu da tsarin ilimin Amurka da kuma yadda yake ƙaunar sa. Ya ce, bambancin dake tsakanin tsarin mulkin Amurka da sauran shine, suna bada damar yaye ɗalibai masu tunani, abin da ya ba su damar mamaye fagen fasaha a duniya.

Ya kuma bada shawarar a samar da ingantaccen tsarin manhajar ilimi da zai ba wa ɗaliban Nijeriya ƙwarewar da ake buqata, don goga kafaɗa da sauran sassan duniya.

A wani labarin kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kai ziyara ga kasuwar wayoyin salula ta Titin Beruit da ke Birnin Kano, inda ya jajanta wa ’yan kasuwar sakamakon iftila’in rushewar bene tare da rasa rai guda. Ya kuma ya ba su gudummawar Naira miliyan 10. 

Can a baya kuma ya bada gudunmawar Naira miliyan 50 ga ’yan kasuwar Kantin Kwari da ambaliyar ruwa ta yi wa ɓarna a Kano.

Wannan dai na ƙunshe ne a bayanin da Abdulrasheed Shehu, Mataimaki na Musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yaɗa labarai ya fitar.