Bikin Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun Juma’a da Litinin masu zuwa a matsayin ranakun hutun gama-gari albarkacin bikin Idil Fiɗir (Ƙaramar Sallah).

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar Muslimi murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara.

Haka nan, ya yi kira ga ɗaukacin Muslimi da su yi koyi da kyawawan halayen da Annabi Muhammad (SAW) ya koyar a halin rayuwarsa.

Daga nan, Aregbesola ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jajirce wajen ganin an miƙa mulki cikin kwanciyar hankali bayan kammala zaɓuɓɓuka cikin nasara.

A ƙarshe, Ministan ya yi fatan al’ummar Muslimi za a yi bikin sallah cikin kwanciyar hankali tare da fatan rahamar Ubangiji ta cimma kowa.