Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Gwamnan Yobe hari

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Wata majiya mai ƙarfi ta ce wasu mahara da ake kyautata zaton Boko Haram sun farmaki ayarin motocin Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni a kan hanyar su daga Maiduguri zuwa Damaturu bayan halartar taron yaye ɗalibai karo na 24 da Jami’ar Maiduguri ta shirya.

Gwamna Buni ya kasance a Maiduguri tare da manyan baƙin da suka halarci bikin, amma daga bisani ya zarce zuwa Abuja domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a can.

Majiya ta tabbatar wa wakilinmu cewa, kwambar motocin jami’an tsaron sun yi arangama da Boko Haram tsakanin Jakana zuwa Mainok a hanyar.

Majiyar ta ci gaba da nuna cewa, “Maharan sun auna motar sojojin da ke jagorantar ayarin motocin da ke ɗauke da MRAP, motar da ke ɗauke da ‘yan sanda da DSS.

“Yayin da hakan ya jawo sojojin mayar da martani mai zafi, al’amarin da ya tilasta wa yan ta’addan ja da baya. Sai dai kuma ɗan sanda ɗaya ya mutu a cikin harin, yayin da kuma sojoji biyu da suka haɗa da direba da ‘yan sanda huɗu sun samu raunuka.”

“Bugu da ƙari, har yanzu ba a tabbatar da adadin asarar rayuka a ɓangaren mayaƙan ba, zuwa lokacin da aka buga wannan labarin.”

“Har wala yau, ayarin motocin jami’an tsaro sun iso Damaturu, babban birnin jihar Yobe lafiya, yayin da aka kwashe waɗanda suka jikkata da direban motar zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin kula da lafiyarsu,” ta bakin majiyar

A nashi ɓangaren, mai magana da yawun Gwamna Buni, Alhaji Mohammed Mamman, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya dage cewa jami’an tsaro uku ne kawai suka samu raunuka, tare da bayyana cewa, ayarin motocin ya isa inda suka nufa, kuma waɗanda suka samu raunuka suna samun kulawar likitoci.