Boris Johnson ya yi murabus daga Firaministan Birtaniya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya sauka daga muƙaminsa na shugabancin jam’iyyar Conservative a daidai lokacin da gwamnatinsa ke fuskantar tangal-tangal.

A cikin wani jawabi da ya yi, Firaministan a ƙarshe ya sanar da shawararsa mai raɗaɗi na yin murabus bayan ya yarda cewa ba zai iya ci gaba da tsayawa ba.

Shekara biyu da kwana 348 da fara shiga ofis a shekarar 2019, Firaministan a yau ya kira Sarauniya ya shaida ma ta cewa yana shirin yin murabus daga muƙaminsa.

Gwamnatin ƙasar dai ta sha fama da ajiye aikin Ministoci da dama.

Boris Johnson dai ya fuskanci matsin lamba ne kan ya sauka daga muƙaminsa, a daidai lokacin da sabuwar Sakatariyar Ilimin ƙasar, Michelle Donelan da Sakataren Arewacin Ireland, Brandon Lewis, suka sauka daga muƙamansu.

Hakazalika, Ministoci Helen Whately da Damian Hinds da George Freeman da Guy Opperman da Chris Philp da kuma James Cartlidge duk su ma sun ajiye muƙaman nasu.

Sai dai Boris Johnson zai ci gaba da zama a kujerar Firaministan har zuwa lokacin da jam’iyyar tasa ta Conservative za ta zaɓi sabon shugaba.

Ana dai zargin Mista Johnson ne da karya dokoki, musamman waɗanda suka shafi yin biki lokacin dokar kullen annobar Korona.

By Editor