Yadda haɗin bakin gidan kurkuku ya sa harin Kuje yin nasara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alamu sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata yadda aka haɗa baki da wasu jami’an tsaro musamman na Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali ta Nijeriya (NCS) wajen samun bayanan sirri a harin yammacin ranar Talata a gidan yarin Kuje, inda mutane biyar da suka haɗa da fursunoni huɗu da jami’an tsaron NSCDC suka mutu.

An kuma tabbatar da cewa jami’an NCS uku sun samu munanan raunuka.
An ce, ’yan ta’addar masu qarfin gwiwa sun yi nasarar gudanar da ayyukansu na tsawon sa’o’i uku tare da samun fursunoni 879 da suka tsere daga ginin.

Cibiyar ta fuskanci munanan hare-haren bama-bamai wanda ya lalata wani yanki mai kyau na ginin da aka ce yana ɗauke da fursunoni aƙalla 1500 da ke zaman gidan yari daban-daban yayin da akasari ke jiran shari’a.

Wata majiya mai tushe ta ce, wasu da ake zargin ’yan tada ƙayar baya sun kai ɗari, inda suka fara tayar da bama-bamai a wurin kafin wasu su fito da yawansu daga wurare da ke kusa da wurin su yi wa jami’an tsaron cibiyar ƙawanya.

Har ila yau, sun yi ta harbin fursunonin da suka nemi tserewa daga ginin inda abun ya rutsa da mutum shida inda ’yan bindigar ke harbe-harbe kan mai uwa da wabi kan duk wani abu da ke motsi ko kuma ake zargin ya tsaya musu a hanya.

Ɗaya daga cikin ’yan jaridar Blueprint da ya ziyarci wurin da aka harin ya afku ya tattaro cewa, wasu sojoji da aka tura muhallin gidan gyaran halin, waɗanda suka kware a harkar tsaro, an fitar da su tare da sake tura su sa’o’i 24 kafin ’yan ta’addan su kai hari gidan yarin Kuje.

Wata majiya mai ƙarfi ta jami’an tsaro da ta san abin da ke faruwa a cibiyar, ta shaidawa jaridar Blueprint cewa, a yayin da aka kwashe sojojin, wasu sabbi ba su iso ba, kafin ‘yan ta’addan su far musu. Wannan, duk da haka, ba a iya tabbatar da shi ba a lokacin wannan rahoton.

Majiyar ta ce, “akwai masu zagon ƙasa a harin Kuje da gwamnati ta yi bincike sosai.” Majiyar da ta ƙi yin ƙarin bayani kan abin da ya bayyana a matsayin ’yan zagon ƙasa, ta yi mamakin yadda ’yan ta’addan suka samu nasarar samun bayanan sirri da kuma shingayen binciken jami’an tsaro ta hanyar amfani da babura.

An kuma tattaro cewa, da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar Talata lokacin da aka shawo kan lamarin kuma aka ɗauki jerin sunayen fursunonin, kusan 111 ne kawai daga cikin kusan 1500 ke wurin.

Sai dai kuma, ya zuwa ranar Laraba da misalin ƙarfe 2:00 na rana lokacin da aka sake yin wani kira, an sake kama wasu sama da ɗari uku da suka tsere ko dai an sake kama su ko kuma da raɗin kansu.

Da ya ke ba da labarin abin da ya faru a lokacin rikicin, Mista John, wani babban ma’aikacin wata hukumar tarayya ya ce, a lokacin da bam na farko ya tashi, mazauna unguwar da ke kusa da su sun yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu, wasu kuma suka tsere zuwa cikin dajin da ke kusa da wani rafi, yayin da wasu kuma suka nemi wurin lavewa.

Ya kuma ce, wasu da dama sun yanke shawarar kwantawa a kasan gadajensu domin gudun kada harsashin ya rutsa da su.

A halin da ake ciki, an rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare da ke cikin birnin Kuje da kewaye yayin da aka buqaci ɗaliban da za su rubuta jarrabawar kammala sakandare da Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta gudanar da su koma gidajensu.

Hakazalika, an buƙaci ɗaliban da ke cikin gidajen kwana na unguwannin da su bar kayansu su koma wurin iyayensu har sai lokacin da hukuma ta samu kan lamarin.

Da ya ke mayar da martani kan harin lokacin da ya ziyarci wurin, Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya ce, dukkan ‘yan ta’addar Boko Haram 64 sun tsere daga wurin.

Magashi ya shaida wa manema labarai cewa, akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa ‘yan ta’adda sun mamaye wurin ne domin su sako mambobinsu da ake tsare da su.

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na aiki tuƙuru domin ganin an kamo sauran fursunonin da suka gudu tare da mayar da su cikin gidan.

Ziyarar Buhari zuwa Senegal

A halin da ake ciki, fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da sukar da wasu suka yi wa tafiyar Buhari ta Dakar.

Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana wannan matsayi, yayin da ya ke gabatar da tambayoyi daga wakilan fadar gwamnati a ƙarshen taron majalisar zartarwa na tarayya na mako-mako a Abuja.

Da ya ke amsa tambaya kan buƙatar da shugaban ya kai ƙasar Senegal don halartar taron ƙungiyar ci gaban ƙasa da ƙasa (IDA) na Afirka, Adesina ya ce, “Eh, ya kamata shugaban ƙasa ya tafi domin akwai taron ƙasa da ƙasa da aka yi nufin shugabanin ƙasashe su halarta. Kada ku ba da kai ga ‘yan ta’adda.

Ƙwararre ya mayar da martani


Da ya ke tsokaci game da fasa gidan yarin, ƙwararre kan harkokin tsaro, kuma jami’in leƙen asiri mai ritaya, Mohammed Bashir, ya ce, harin da aka kai a gidan yarin Kuje ya wuce ƙarfin da gwamnatin Nalijeriya ke da shi na tabbatar da tsare fursunonin yadda ya kamata.