Duniyar ce ta sauya ko mutanen cikinta?

Assalamu alaikum. Tarbiyyar yara a wannan lokacin ta wuce a ce iyaye ne kawai za su kula da ita, zamani ya zo na sauyin rayuwa, yara da manya kowa ya san kuɗi kuma ya san inda ake kashe su, savanin shekarun baya da muka samu labarin cewa wani sai ya haura shekaru goma sha biyar ba ya kashe kuɗi da kansa sai dai in aikensa aka yi sayen wani abu.

A zamanin iyaye da kakanni ana rayuwa ne ba tare da dogon buri ko hangen wani ya fini ba, mutum mai wadata yana iya riƙe yaran maƙotansa da sauran yaran ’yan uwansa, karatunsu, cinsu da shansu duk yana wuyansa, sannan a wancen zamanin idan ka samu yaro komai ƙanƙantarsa yana ɗaukar kowanne mutum a matsayin babansa, za ka gansa babban gida mai mutane da yawa amma mutum ɗaya ne ya ke ɗaukar nauyin komai na su, hatta aure idan ya kama shi ne zai yiwa yaransu, idan wani babba a gida ya hana a yi wani abu to fa komai rintsi babu wanda zai buɗa baki ya ce a yi.

A wancan lokacin ba sai wanda ku ke gida ɗaya ne zai tsawatar da kai don ka yi wani abu ba, hatta mutum yana tafiya akan hanya idan ya ga yara sun yi abu mara kyau zai dakata ya hana su tare da yi musu faɗan karsu qara, idan ta kama da duka ma zai doke su, uban yaron da aka doka ba zai ce komai ba idan ya zo ya tarar sai ma ya yi godiya akan abin da aka yiwa yaron nasa.

Me ya sa yanzu aka daina hakan?

Zamani ne ko kuma mutnen ne suka sauya? Duniyar dai tana nan yadda ta ke komai bai sauya ba sai dai mu ne muka sauya.
Za ka ga mutum, ya kai wani mataki na rayuwa amma ya bar wasu daga makusantansa a wani hali, babu batun baiwa yaransu kulawa, balle idan ‘ya’yan ƙannensa ko yayyensa sun shiga maraici ya ba su kulawa.

Duk da kamar yadda na faɗa a sama, zamanin ne ya zama abin tsoro, mutum na jikinka wanda ka janyo shi ku ke yin harkoki wasu da su ake haɗuwa a cutar da kai, batun yara kuma yanzu komai ƙanƙantar yaro in dai ya fara tafiya zuwa fita waje to za ka sha mamakin yadda ya san kuɗi harma da yadda zai kashe su, wannan ne ya sa hatta yaran da mutum ya haifa ya ke tsoron su shiga jikinsa sosai musamman idan shi ɗin mai dukiya ne.

Sannan abu na gaba a wannan zamani shi ne, kowanne mutum bai yarda cewa wani zai iya bai wa yaransa kulawa ba, za ku yarda da ni idan kuka duba yadda iyaye suke yi a yanzu, yaro zai yi laifi da zarar wani ya tsawatar da shi, to fa abin zai zama laifi, wani ma idan ɗansa ya yi laifi aka daki yaron, to ƙarshe sai dai ku rabu a gurin hukuma idan ma bai ce zai rama wa yaron ba.

Yaron da aka ce na kowa ne yanzu yara sun koma na iyayensu kawai, basu yarda su kira wani baba in ba wanda ya haifesu ba, ba su ɗaukar faɗan kowa sai na iyayensu.

Wannan ya sa yanzu rayuwar ta lalace, maƙoci zai ɗauki gaba da makocinsa saboda yara, za ka samu mazaje a gida ɗaya suka taso wa da ƙane sun yi rayuwa mai kyau, ba su taɓa faɗa ba amma akan yara sai gaba ta shiga.

Me hakan zai haifar?

  1. Haifar da sata gurin aananun yara, za ka samu ƙaramin yaro yana ɗaukar kuɗi a gida yana ƙashewa a waje.
  2. Daga nan zai fara ɗaukar na maƙota, hakan zai ba shi damar sayen abubuwa na more rayuwa, wanda a gida idan ya zo da su babu mai tambayarsa inda ya samu.
  3. Daga nan kuma girma ya fara binsa ƙarfin samartaka za ta sa ya fara hangen yin wani abu na gayu, hakan zai sa satarsa ta hauhawa zuwa ƙwacen waya wanda kusan shi ne abu mafi muni da ake ta fama da shi yanzu, an rasa ta inda za a magance hakan, mutum idan ya fita yana tsoron yadda zai yi ya koma gida da wayarsa, wasu ma a gida su ke barin wayar saboda tsoro. Ƙaramin yaro zai zare wuƙa ya ce, bani waya.

Allah ya sa mu dace, Ilahi.

Daga Mustapha Musa Muhammad ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.