Buhari ya umarci ministocinsa masu son takara su yi murabus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci ministocinsa masu son takara su yi murabus daga nan zuwa 16 ga watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ne ya sanar wa da manema labarai hakan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa na mako-mako a ranar Laraba da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Daga cikin ministocin da hakan zai shafa akwai Rotimi Amaechi Ministan Sufuri da Chris Ngige Ministan Ƙwadago da Abubakar Malami Ministan Shari’a da kuma Godswill Akpabio Minsitan Ma’aikatar Harkokin Kula da Neja-Delta.

Dukkan waɗanda ministoci sun nuna sha’awar tsayawa ko dai takarar gwamna ko ta sanata ko ta shugaban ƙasa.

Tun da fari a ranar 25 ga watan Fabrairun 2022 Shugaba Buhari ya buƙaci ‘yan majalisa tarayyar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu riƙe da mukaman gwamnati jefa ƙuri’a a zaɓen shugabannin jam’iyya ko kuma na ‘yan takara.

Shugaban ya nemi hakan ne a lokacin da ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓe ta ƙasar wadda aka ɗauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kanta.

Sai dai ‘yan majalisar dokokin ƙasar sun yi watsi da buƙatar Shugaba Buhari na cire wani sashe daga sabuwar dokar zaɓe, inda tun a lokacin alamu suka nuna cewa wasu daga cikin ƙusoshin Gwamnatin Tarayya da na jihohi na cikin ruɗani.

Dukkanin zaurukan majalisun tarayyar biyu, ta wakilai da ta dattawa sun qi amincewa da gagarumin rinjaye su gyara Sashe na 84(12) da ya tanadi cewa wajibi ne masu riƙe da muƙaman siyasa su ajiye aikinsu kafin su iya jefa ƙuri’a a zaɓen jam’iyyu ko kuma a zaɓe su.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci Buhari, da Babban Lauyan gwmnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan kar su sauya sashen dokar.

Da yake bayar da umarnin a ƙarar da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta shigar, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce dokar zaɓen ta zama cikakkiyar doka kuma ba za a iya sauya ta ba tare da bin tsarin doka ba. Sai dai Ahmad Lawan ya ce kotun ba za ta hana su yin aikinsu na majalisa ba.