27
Dec
Daga Umar Mohammed Gombe a Abuja Duk da cewa kusan kowane dan Adam yana buqatar wurin da babu hayaniya don debe kewa ko samun hutu ko nishadi, amma labarin ya kan sauya da zarar mutum ya shiga cikin wani daki, wanda aka yi ittifaqin ya fi kowane daki shiru a Duniya. Dakin mafi ban al'ajabi da ake masa laqabi da 'Anechoic Chamber' ya kasance ne a birnin Minnesota na Qasar Amurka, wanda wani attajiri Steven Orfield ya gina don aiwatar da gwaje-gwajen fasahar software. Jaridar Daily Mail ta Amurka, ta ruwaito cewa tsananin shirun dakin ya kai miqdarin maganadisun ma'aunin…
