Rahoto

Kano 2023: Za mu inganta ilimi da yashe dam-dam a Jihar Kano – Balarabe Rufa’i

Kano 2023: Za mu inganta ilimi da yashe dam-dam a Jihar Kano – Balarabe Rufa’i

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano A cigaba da zagayawa, don ƙara neman goyon bayansa ga al'ummar ƙananan hukumomi 44 da suke Jihar Kano, ɗan takarar kujerar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Balarabe Rufa’i, ya alƙawaranta cewa, idan ya samu nasara zai inganta harkar ilimi da yashe dam-dam da ke akwai a jihar don inganta harkar noma da sauransu. Ya ce babu abinda ya fi a yanzu face matasa da sauran al''umma su tashi tsaye don zaɓar wanda zai kawo masu cigaba da canje-canje don cigaban yankinsu da rayuwarsu. Ɗan takarar gwamnan ya kuma ƙudurci…
Read More
Ɗan Bafarawa, mai neman kujerar Gwamnan Sakkwato a PDP, ya tsallake rijiya da baya

Ɗan Bafarawa, mai neman kujerar Gwamnan Sakkwato a PDP, ya tsallake rijiya da baya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Mai son tsayawa takarar gwamnan Sakkwato a tutar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 kana ɗa ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sagir Attahiru Bafarawa ya tsallake rijiya da baya ne bisa ƙoƙarin hallaka shi da wasu da ake zargi ɓatagari ne da yunƙurin yi a Sakkwato. A wani bayani da dandalin goyon bayan Sagir Bafarawa suka fitar, sun bayyana cewa wani sanannen ɓatagari a Sakkwato Alu KC ne suka dirar wa gidan Sagir da nufin hallaka shi jim kaɗan bayan kammala sallar Taraweeh a daren ranar Talata wanda ya tsallake rijiya da baya a lokacin. “Yau…
Read More
Gwamnatinmu ta samar da tsaro fiye da wacce mu ka gada – Buhari

Gwamnatinmu ta samar da tsaro fiye da wacce mu ka gada – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana cewa gwamnatinsa ta fi samar da tsaro a kan lokacin mulkin Goodluck Jonathan. Buhari ya bayyana hakan ne a taron Kwamitin Ƙoli na Ƙasa na APC da ya gudana Laraba a Abuja. Premium Times ta rawaito cewa Buhari ya ce yanzu an fi samun matsalar tsaro a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda ya ce Arewa maso Gabas ta samu zaman lafiya yanzu.  Sai dai kuma shugaban ya tabbatar da cewa zai yi amfani da irin salon da ya yi na yaƙar Boko Haram a…
Read More
Muna zaman lafiya da sauran ƙabilun garin Legas, inji Wazirin Obalande

Muna zaman lafiya da sauran ƙabilun garin Legas, inji Wazirin Obalande

Daga DAUDA USMAN USMAN a Legas An bayyana cewa a halin yanzu al'ummar Hausawa mazauna garin Legas ba suda wata matsala a tsakanin su da sauran ƙabilu mazauna Jihar Legas. Hakan ya fito ne daga bakin Wazirin Marigayi Malam Adamu, Sarkin al'ummar Hausawan Obalande da ke Legas, Alhaji Salisu Mohammed Malam Madori, jim kaɗan bayan buɗe bakin azumi a ƙarshen makon nan. Malam Madori ya ƙara da ce, "haƙiƙa an samu kyakkyawar zamantakewa tsakanin sauran ƙabilu da Hausawa mazauna garin Legas, inda muke ƙara samun fahimtar juna, wanda har auratayya ana yi a tsakani a yankin Obalande." Ya yi addu'a…
Read More
Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babban Hafsan Sojin Sama na Nijeriya, Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin jirgin sojin sama mai ƙirar 401 ya faru don jajenta wa dangin mutane biyun da suka rasa rayukansu. Jirgin dai ya faɗo ne a Kaduna da yammacin Talata a wani sansanin sojan sama a Kaduna. a lokacin da ya ziyarci Kaduna ranar Larabar da ta gabata don jajenta wa iyalai, abokai da 'yan uwan matuƙa jirgin saman da ya faɗo a Kaduna mai ƙirar 401 na makarantar koyon tuƙin jirgi, inda ya tabbatar da cewa an ɗauki dukkan…
Read More
Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Daga UMAR GARBA a Katsina Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu ya ajiye muƙaminsa na kwamishinan ma'aikatar aikin gona, muƙamin da yake riƙe da shi tun kimanin shekaru 7 da su ka wuce a bisa jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari. Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Musa Kalla ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai jiya Alhamis. Kalla ya bayyana cewar mataimakin gwamnan ya ajiye muƙamin nasa ne don bin umarnin sabuwar dokar zaɓe da shugaban ƙasa ya saka wa hannu mai lamba 84(12) ta shekarar 2022 wadda aka gyara. Ya ƙara…
Read More

Dalilinmu na ƙin tura jirgin yaƙin Tucano Arewa Maso Yamma – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta bayyana cewa, kafin a aike da jiragen saman yaƙi na Tucano da aka sayo daga Amurka a yankin Arewa Maso Yamma, wanda ’yan bindiga suka mamaye, akwai buƙatar a bi ƙa’idojin sayen jiragen, domin kada Nijeriya ta kasance cikin baƙin littafin Ƙasar Amurka. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da wani shiri a gidan talabijin na Trust. ’Yan Nijeriya 43,000 ne za su samu damar yin aikin hajjin 2022 “Sojojinmu ƙwararren soja ne. Shugaban ƙasa ne…
Read More
Ayyukan mazaɓu: Yadda wasu sanatoci suka yi sama-da-faɗi a mazaɓunsu – Rahoto

Ayyukan mazaɓu: Yadda wasu sanatoci suka yi sama-da-faɗi a mazaɓunsu – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta yi cikakken bayani kan yadda ake zargin wasu sanatoci guda uku daga jihohin Kebbi, Taraba, da Jigawa da sama-da-faɗi da kuɗaɗe a ofishinsu tare da mayar da kadarorin jama’a zuwa ga amfanin kansu wajen gudanar da wasu ayyukan mazaɓu na miliyoyin naira. A cewar hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, ’yan majalisar sun bada kwangilar gudanar da wasu ayyukan mazaɓu da suka gabatar wa gwamnati inda su, danginsu ko abokan hulɗarsu ke da muhimmin kaso kai tsaye ko a kaikaice. “A…
Read More
PDP 2023: Baki ya zo ɗaya a tsakanin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya

PDP 2023: Baki ya zo ɗaya a tsakanin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike a ranar Laraba da ta gabata ne tare da sauran masu neman tsayawa takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP suka yi wata ganawar sirri a tsakanin su a gidan gwamnatin Ribas dake garin Fatakwal. Waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, takwaran sa na Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dokta Abubakar Bukola Saraki, da kuma tsohon shugaban bankin FSB International Bank, Dokta Mohammed Hayatu-Deen. Da yake yi wa manema larabai jawabi jin…
Read More
Gwamna Buni zai tallafa wa matasa 300,000 da kayan sana’a don dogaro da kai

Gwamna Buni zai tallafa wa matasa 300,000 da kayan sana’a don dogaro da kai

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sanar da ɗaukar matakin taimaka wa matasan jihar 300,000 da tallafin sana'o'i don samun abin dogaro da kai tare da yaƙi da talauci a jihar. Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a lokacin da al'ummar jihar suka shirya masa gagarumar tarba a babban filin wasa na 27 August Stadium, domin taya shi murnar kammala babban taron jam'iyyar APC a matsayin sa na shugaban riqo kimanin shekaru biyu. A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya sha alwashin tallafa wa matasa a faɗin jihar da Keke Napep don inganta rayuwar su…
Read More