Gwamnatinmu ta samar da tsaro fiye da wacce mu ka gada – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana cewa gwamnatinsa ta fi samar da tsaro a kan lokacin mulkin Goodluck Jonathan.

Buhari ya bayyana hakan ne a taron Kwamitin Ƙoli na Ƙasa na APC da ya gudana Laraba a Abuja.

Premium Times ta rawaito cewa Buhari ya ce yanzu an fi samun matsalar tsaro a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda ya ce Arewa maso Gabas ta samu zaman lafiya yanzu. 

Sai dai kuma shugaban ya tabbatar da cewa zai yi amfani da irin salon da ya yi na yaƙar Boko Haram a Arewa maso Gabas wajen samar da zaman lafiya a Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Gabas.

Manhaja ta rawaito cewa Buhari ya yi iƙirarin ne yayin da ‘yan fashin daji, ISWAP da IPOB ke cin karensu ba babbaka a ƙasar nan, inda a kulli-yaumin a ƙasar ake samun rahoton kashe-kashe da munanan kai hare-hare.