Rahoto

Kisan mace da yaranta a Anambara dabbanci ne, cewar Sarkin Musulmi

Kisan mace da yaranta a Anambara dabbanci ne, cewar Sarkin Musulmi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Shugaban Majalisar Ƙoli a kan Lamurran Addinin Musulunci a Nijeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya nuna damuwa akan abinda ya faru a Jihar Anambara na kisan Harira da yaran ta uku. Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo yayin wata ziyarar neman goyon bayan wakillan jam'iyyar APC da ke Sakkwato da za su kaɗa ƙuri'un zaɓen wanda zai tsayawa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 wato daliget. "Abinda ya faru a jihar Anambara, abu ne na dabbanci na kisan mace…
Read More
Harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja: Mahara sun aika saƙo ga Gwamnatin Nijeriya 

Harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja: Mahara sun aika saƙo ga Gwamnatin Nijeriya 

Daga AMINA YUSUF ALI Watanni biyu kenan bayan da wasu mahara suka kai wani mummunan hari ga fasinjojin jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja wanda aka kai harin Karatu ranar 28 ga watan Maris, 2022. Harin wanda aka shirya shi tsaf kafin a gudanar da shi ya yi sanadiyyar mutuwa da raunana fasinjoji da dama, da jirgin kansa da kuma ita kanta gadar jirgin. Sannan kuma uwa uba an yi garkuwa da mutane da dama. Waɗannan mutane da aka ɗauke sun shafe bikin Ista, Azumin watan Ramadan da Sallah ƙarama dukkan a hannun waɗannan 'yan bindiga. Kodayake, tun a kwanakin baya ne…
Read More
Ku kawo ƙarshen yajin aikin ASUU ko ku fuskanci bore – Gargaɗin Shugaban ɗalibai ga gwamnati

Ku kawo ƙarshen yajin aikin ASUU ko ku fuskanci bore – Gargaɗin Shugaban ɗalibai ga gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), Sunday Asefon ya bayyana cewa, ɗaliban Nijeriya sun shirya tsaf domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shiga. Shugaban ɗaliban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 5 ga Mayu, 2022 yayin da ya ke magana a wani shirin gidan Talabijin na Channels mai suna 'Sunrise Daily'. A cewar Sunday Asefon, da alama gwamnati ba ta da niyyar kawo ƙarshen yajin aikin, ganin yadda aka karkata akalar zaɓe a shekarar 2023. Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki bayan da…
Read More
Manema labarai bakwai suka rasa rayukansu tsakanin 2015 zuwa 2022 – Gidauniyar MFWA

Manema labarai bakwai suka rasa rayukansu tsakanin 2015 zuwa 2022 – Gidauniyar MFWA

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Manema labarai bakwai ne suka halaka, yayin da aka ci zarafin waɗansu guda 300 a cikin tashin-tashina da suka jivanci ‘yan jarida guda 500 a Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa Afrilun 2022, kamar yadda rahoton Gidauniyar Kafafen Watsa Labarai ta Afrika ta Yamma (MFWA) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) suka fitar. Zamani ko lokacin wannan nazari ya haɗa da wa’adin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, la’akari da cewar wa’adin mulkin sa ya fara ne tun daga shekara ta 2015, domin ya sava rantsuwar kama aiki a watan Mayu na wancan shekarar. Rahoton, wanda aka…
Read More
Zan bada gudunmuwa wajen kawo cigaban ‘yan Arewa mazauna Legas – Hajiya Amina

Zan bada gudunmuwa wajen kawo cigaban ‘yan Arewa mazauna Legas – Hajiya Amina

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugabar mata ta ƙungiyar 'Arewa Community' da ke jagorantar shiyya yammacin Legas, Hajiya Amina ta sha alwashin yin iyakacin ƙoƙarinta tare da bada gudunmuwa wajen kawo cigaba mai ma'ana ga al'ummar Arewacin Nijeriya mazauna Jihar Legas. Hajiya Amina ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar gaisuwar azumi da ta kai wa shugaban ƙungiyar na jihar, Alhaji Sa'adu Yusuf Dandare Gulma a ofishin sa ranar Lahadin da ta gabata. Ta ce za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta haɗa kan al'ummar shiyyar da take shugabanta, musamman wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna a…
Read More
Aisha Buhari ta yi wa ’yan Zamfara addu’a

Aisha Buhari ta yi wa ’yan Zamfara addu’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan Shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al'ummar Jihar Zamfara taddu'ar zaman lafiya. Aisha Buhari ta wallafa saƙon ne da misalin ƙarfe 12:09 na daren Laraba, inda ta roƙi Allah ya samar wa mutanen jihar da sauran 'yan ƙasar mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a lokacin da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Ƙadri: "Allah ya fitar da mu da mutanen Jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Ƙadri, Ameen!" Baya ga saƙon,…
Read More
Harin jirgin ƙasa: Kanar Ɗangiwa ya nemi agajin ƙungiyoyi wajen ceto rayuka

Harin jirgin ƙasa: Kanar Ɗangiwa ya nemi agajin ƙungiyoyi wajen ceto rayuka

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon gwamnan mulkin soji na Jihar Kaduna, Kanal Abubakar Ɗangiwa Umar (ritaya), ya miƙa kokensa na bara ga al’ummomin duniya, musamman kwamitin ƙasa da ƙasa ta ‘Red Cross’ (ICRC) da ta taimaka ta shiga cikin shawarwari na wakilci da zummar ceto fasinjoji dake cikin jirgin ƙasa wanda yau kimanin wata guda kenan yana kan hanyar sa zuwa garin Kaduna ‘yan ta’adda suka yi masa farmaki. Wannan kira na tsohon gwamnan, ya biyo bayan kasancewar sa dangi kuma ɗan uwa ga wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan da aka kai wa farmaki, kamar yadda ya zayyana…
Read More
Matar da aka sace a harin jirgin ƙasa ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Matar da aka sace a harin jirgin ƙasa ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗaya daga cikin fasinjojin da 'yan fashin daji suka sace daga jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.Tashar talabijin ta AriseTV, wadda ta wallafa wannan labarin, ta kuma ce wani ɗan uwan matar ne ya sanar da su haka. Ɗan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake riƙe da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa. "Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gwamman…
Read More
Fadar Shugaban Ƙasa ta gaskata afuwar da aka yi wa Dariye da Nyame, cewar Garba Shehu

Fadar Shugaban Ƙasa ta gaskata afuwar da aka yi wa Dariye da Nyame, cewar Garba Shehu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Fadar Sugaban Ƙasa ta gaskata afuwar shugabanci da aka yi wa tsoffin gwamnoni Joshua Dariye da Jolly Nyame, tana mai faɗin afuwar ta biyo bayan tanade-tanaden dake cikin kundin tsarin mulkin ƙasa ne. Fadar ta kuma bayyana cewar, afuwar ba ta yi tsaiko ko karan-tsaye wa yaƙi da rashawa da cin hanci ba, har ila yau an zaƙulo tsofaffin gwamnonin ne da zummar yi masu afuwa bisa la’akari da yanayin lafiyar su. Tun makon da ya gabata, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayyana cewar, an yi wa ‘yan Nijeriya kimanin…
Read More
Ku ba mu Naira miliyan 200 cikin kuɗin tallafin fetur – ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Ku ba mu Naira miliyan 200 cikin kuɗin tallafin fetur – ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHNAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa ɗaliban jami’o’in gwamnatin Nijeriya suke zaune a gidajensu. A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kuɗin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu ba ta ce komai ba akan ilimin jami’o’inta. Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kuɗin kasafin tallafin man fetur, Naira tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira tiriliyan 3.8 wurin kawo ƙarshen matsalolin jami'o'i.…
Read More