Manema labarai bakwai suka rasa rayukansu tsakanin 2015 zuwa 2022 – Gidauniyar MFWA

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Manema labarai bakwai ne suka halaka, yayin da aka ci zarafin waɗansu guda 300 a cikin tashin-tashina da suka jivanci ‘yan jarida guda 500 a Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa Afrilun 2022, kamar yadda rahoton Gidauniyar Kafafen Watsa Labarai ta Afrika ta Yamma (MFWA) da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) suka fitar.

Zamani ko lokacin wannan nazari ya haɗa da wa’adin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, la’akari da cewar wa’adin mulkin sa ya fara ne tun daga shekara ta 2015, domin ya sava rantsuwar kama aiki a watan Mayu na wancan shekarar.

Rahoton, wanda aka fitar a birnin tarayya ta Abuja a makon da ya gabata, ya bayyana cewar, wannan sauyi wani babban abin takaici ne dubi da yadda ‘yan jarida da kafofin yaɗa labarai suka kasance mahara ko maƙasudi wa masu zanga-zanga da gwamnati.

Babban daraka a cibiyar fafutukar neman ‘yancin walwala da ilimin tattalin arzikin jama’a wato ‘Citizen Advocacy for Social and Economic Right’ (CASER), Frank Tietie wanda ya gabatar da rahoton, ya ce wannan bahagon sauyi ya mayar da tunani baya zuwa lokutan mulkin soji, lokacin da kafofin watsa labarai a Nijeriya suka sha tasku.

“Ƙasar tana fuskantar wani yanayi dake neman tozarta ko rage sana’ar neman labari ko aikin jarida da hukumomin gwamnati da masu zaman kan su suke yi,” a cewar Tieti.

“Njeriya tana cigaba da zama gagarabadau wajen gazawar ta na cin kare babu babbaka da ake yi wa manema labarai, har ma da yi masu kisan gilla.

“Misali, a shekara ta 2017, manema labarai guda huɗu aka kashe a wasu yanayi daban-daban, ba tare da an yi bincike domin gano masu aikata laifi ba, da gano manufar su da aikata irin wannan taɓargaza.

“Manema labaran guda huɗu da suka sheƙa barzahu su ne Ikechukwu Onubogu, wani mai ɗaukar hotuna wa gidan talabijin na jihar Anambra; Lawrence Okojie na Gidan Talabijin Tarayyar Nijeriya (NTA) dake jihar Edo; Famous Giobaro, wani mai tace labarai dake gidan rediyon ‘Glory FM’ a jihar Bayelsa; da kuma wani ɗan jarida mai zaman kan sa, Abdul Ganiyu Lawal dake jihar Ekiti.

A cewar Tietie, kaiwa farmaki wa kafofin watsa labarai wata alama ce ta gurguwar dimokraɗiyya da gwamnati maras haƙuri.

Ya ƙara da cewar, “abu ne na fahimta cewar, samun ‘yanci da fayyataccen aikin jarida wani ginshiqi ne ko tubali na assasa dimokraɗiyya da cigaban jama’a, waɗanda ya kamata su samu tagomashi da ƙarfafawa.”

Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida a mataki na ƙasa (NUJ), Chris Isiguzo ya ji takaicin yawan farmaki da ake kai wa manema labarai a faɗin ƙasar nan.

Isiguzo ya bayyana cewar, “kwanciyar rai ko hankalin manema labarai ta zarce guje wa yi masu kisan gilla ko duka, ta haɗa da guje wa yawan tsare su, gudun hijira domin guje wa kisa, ƙuntatawa, haɗi da ɓarnata ko ƙwace kayayyakin aiki da matsugunai.”

Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida dake babban birnin tarayya, Abuja, Mista Emmanuel Ogbeche sai ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa yin aiki tare da juna a tsakanin su domin tabbatar wa kawuwanan su ‘yancin zaƙulo labarai a duk saƙo, lungu ko kwazazzaban ƙasar nan da labarun suke maƙare.

Ya bayyana cewar, ƙungiyar za ta cigaba da goya baya wa yaƙi da nuna ƙarfi fiye da kima da ake yi wa manema labarai a Nijeriya.