A ina masallacin Al’aƙsa ya ke?

A wani yanayi da ya ke faruwa a gabas maso yammacin Asiya, wanda ana samun rashin jituwa tsakanin ƙasashen Larabawa ta Falastin da kuma Yahudawa an Isra’ila. Mutane da dama suna rasa rayuwarsu, musamman yara ƙanana da mata, da kuma tsofofi da likitoci sai kuma ’yan jaridu.

Massallcin Al’aƙsa an gina shi ne akan wani tsauni a Jerusalem ko Ƙuds da Larabci. Wuri na uku kenan a duniya da suka fi tsariki a duniyar musulunci. Wanda daga Ƙa’aba da ke Makka sai kuma Masallacin Annabi (S) da ke birnin Madina. Al’aƙsa yana kudu maso gabashin tsohuwar birnin Kudus. Ana wa masalacin laƙabi da Masjidil Haram  mai tsarki. An ambaci Masallacin a cikin littafin Ƙur’ani mai tsarki, sai dai wasu na ganin akwai shakku, domin wurin da Ƙur’ani na nufi kamar baizo daidai da muhallin da Kudus ya ke a yanzu ba.

Ana iƙirarin cewa Masallacin ya samo asali ne daga Addinin Ibrahimawa 3, ko muce akwai addinai sama da 3 da suka yarda da msallacin a matsayin wurin Ibadansu ne mai tsarki. Kamar Addinin Yahudanci, da kuma Kiristanci da kuma addanin Musulunci. Duk wayan nan addinan sun yi ikirarin cewa wuri ne mai tsarki a wurin su. Dukkan su sunyi imanin cewa muhalli ne na ibada zuwa ga Allah. 

Masallacin yana iya ka da ƙasar Israila, da kuma Banki yamma ta Fakastin. Kamar yadda na faɗa a sama, dukkan ƙasashen biyu kowa yana ikirarin cewa Jerusalem ita ce babban birninsu.

Tun a farko-farkon ƙarni na 19,  gabas maso kudancin na masu addinin Yahudanci ke da wurin, sun ɗauki kaso 1 bisa 4, sai kuma masu addini Armaniya, sun ɗauki 1 bisa 4, sai kuma masu bin Addinin Kisirtanci suma 1 bisa 4, yayin da suma musulmai ke 1 bisa 4. 

Kamar yadda na yi bayani a farko, kowanne Addinin yana ikirarin cewa Masallacin na shi ne. Kuma duk wanda   yaje wajen sai ya yi sallah.

A littafan musulunci, tarihi ya nuna cewa, Masallacin Al-Aƙsa bai samu ci gaba ba sai a lokacin halifancin sarakunan Biliyaminu guda biyu, wato Abdulmalik bin Marwan da dansa Walid bin Abdulmalik. Kuma ana kiransa da ‘Harami Mai Tsarki’. A shekara ta 691 miladiyya, Abdul Malik Ibn Marwan ya gina masallacin Al-Aƙsa a yankin da ya ke a yanzu kuma ya gina gininsa mafi muhimmanci da ake kira Dome of the Rock.

A zamanin mulkin Walid bin Abdulmalik, an ci gaba da gina masallacin Al-Aƙsa da raya shi, wanda ya haɗa da baranda guda 7, da baranda 1 a tsakiya, da baranda 6 a ɓangaren yamma da gabas na masallacin. Haka nan masallacin Al-Aqsa yana da ƙofofi 11 a cikin wannan lokaci, 7 daga cikinsu suna Arewa, 1 a gabas, 2 a yamma, 1 a kudu. Domin samar da ruwa mai tsafta ga masu ibada, an haka rijiyoyi 25 tare da shirya wani ƙaramin tafki domin yin alwala a gaban masallacin. A cikin waɗannan lokuta, an qara wuraren shan ruwa guda 2 a cikin masallacin.

Masallacin Al-Aƙsa ya ruguje sakamakon girgizar qasa a shekara ta 747 miladiyya da kuma a shekara ta 1033.

 miladiyya kuma Mansour Khalifa Abbasi ne ya sake gina shi. Babban harsashin masallacin Al-Aƙsa ya samo asali ne tun zamanin sarakunan Umayyawa biyu, wato Abdulmalik bin Marwan da ɗansa Walid bin Abdulmalik.

Sai dai akwai shakkun cewa wannan ayar ta Ƙur’ani ba tana magana ne a kan masallacin Al-Aƙsa da ake  a halin yanzu ba, kuma wasu malaman na ganin mai yiwuwa Ƙur’ani ya yi nuni da masallacin Al-Aƙsa a matsayin wani wurin a Aljanna, wanda yayi daidai da sunan wannan masallacin. Mai yiwuwa ya samo asali ne daga farfagandar ‘yan Biliyaminu a zamanin Abd al-Malik bn Marwan, wanda ya tayar da Kudus don rage muhimmancin Makka, domin Makka tana ƙarƙashin mulkin Abdullahi bn Zubair, wanda ya kasance mai adawa da Banu Umayyawa.

Tahirin musulunci ya nuna cewa, Masallacin Al-Aƙsa yana ɗaya daga cikin mafi tsarkin wuraren Musulunci ga Musulmi. Misali a wasu hadisan Ahlus-Sunnah sun ce wannan masallaci shi ne harami na uku bayan masallacin Harami da masallacin Nabi da ke Makka da Madina. An gina Haramin ne bisa umarnin Allah.

Sai dai wasu hadisai a littafan ya sha bamban, musamman a littafan Shi’a. Suna ganin falalar masallacin Al-Aƙsa bayan masallacin Kufa ne dake Iraki. A cikin littafin Wasa’il Al-Shi’ah akwai babi mai suna ‘Mustahabbi ne a zauna a masallacin Kufa a yi salla a cikinsa, idan aka kwatanta da tafiya ziyarar masallacin Al-Aƙsa’.

Da farko Isra’ila ta ayyana gobarar a matsayin wanda ta tashi ba da niyya ba saboda katsewar wutar lantarki. Kwamitocin bincike sun tabbatar da cewa da gangan ne hakan ya sa Isra’ila ta sauya matsayinta tare da xora laifin gobarar da ta tashi a kan Michael Rohan ɗan ƙasar Australia. Da farko Isra’ila ta kama Rohan, amma daga baya sakeshi ta mayar da shi Ostiraliya.

Rikici dai ya ci gaba da faruwa, kamar yadda ko wanne ƙasashen biyu, da Isra’il da Palestine suna ikirarin cewa birnin ta Ƙudus ɗin nasu ne. Wannan nema na daga cikin babban dalilinda ya sa aka samu samu jituwa tsakanin su.

Aƙalla ana shafe sama da shekaru 60 kenan a na rikici, wanda ya zama tamkar na Addini a gefe guda kuma zaka fahimci cewa ba na Addini bane, kamar ƙabilacin ne, tsakanin Yahudawa da kuma Larabawa. Amman zahirin gaskia, akwai hannun ƙasashen yammacin duniya, domin tin bayan yaƙin duniya na 2, a shekara ta 1947, Majalisar cikin duniya ta amince da raba kan Falastin zuwa ƙasashe kamar haka, ƙasar Isra’il, da kuma ƙasar Falastin, sai kuma Kudus. Su kuma Falastinawa basu yarda ba, ya za a yi a ce an raba musu ƙasarsu, bayan daman can a baya babu Israel a hankin.  

Ba da daɗewa ba duk membobin ƙungiyar Larabawa suka amince da hakan, amman ban Jodan, wanda ya mamaye kuma daga baya ya mallake Yammacin Kogin Jodan da ke  gabashin Jerusalem ɗin.  

Wannan shi ne a taƙaice, game da Masallacin Al’aƙsa, da kuma abubuwan da ke faruwa a yanzu. Allah ka tausaya mana, ka kuma bamu zaman lafiya, Ameen ya Allah.

Saƙo daga Mohammed Albarno, O8034400338, [email protected]