Umurnin Buhari na sake buɗe iyakoki

A yau ma shawara ce wacce ba bu tilas a ciki. A makon jiya ne umurni ya zo daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a kan sake buɗe wasu iyakokin ƙasa wadda ta raba iyakokin jamhuriyar Nijer da ƙasarmu Nijeriya.

Tun rufe ta wasu ke ta ƙorafe-ƙorafe iri iri tare da fatan a sake buɗe ta. An ce a sake buɗe ta amma har yau wasu na cewa siyasa ce. Tabbas iya ma mutane sai Allah amma kar mu manta duk abinda shugaba zai aiwatas ba dole yai ma kowa daidai ba kuma ita doka idan ba a binta kai da ni duka da mun shiga uku a rayuwa. Shawara ta ita ce, kar bambancin siyasa ko wata manufa ta zamo maƙamin yaƙar duk umurni ko hani na mai shugabanci ganin yadda mun sani cewa ko a gidan mutum sai an ɓata ma wasu kafin a gyara ma wasu domin mu mutane ba duka kowa ke son ai gyara ba. 

Allah ya taimaki shugabanninmu wajen aiwatar da adalci a gare mu.

Wasiƙa daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519, 08080140820.