Elon Musk ya saye Tiwita kan fiye ninkin dukiyar Ɗangote

Daga AMINA YUSUF ALI

Mutumin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya samu damar mallakar kamfanin Tiwita akan farashin Dalar Amurka biliyan $44, fiye da ninkin biyu na dukkan arzikin da ma fi kuxi a Afirka, Aliko Dyangote ya mallaka. 

Kamar yadda jadawalin biloniyoyi na jaridar Ingilishi ta Bloomberg ya bayyana, a yanzu haka dai ƙarfin arzikinsa da ke Amurka biliyan $20.4 ne. Kuma shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Afrika, kuma na 72 a Duniya.

A hannun guda kuma shi Elon Musk shi ne na ɗaya a arziki a Duniya kuma ƙarfin arzikinsa ya kai Dalar Amurka biliyan $259.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai kamfanin Tiwita ya tabbatar da cewa ya sayar wa da Musk Kamfanin a kan Dalar Amurka biliyan $44 wato fiye da ninkin biyu na arzikin Ɗangote.

Wannan ciniki an yi shi ne bayan an yanke wasu manyan mahukunta kamfanin a sanbga. Domin a da ba su so cinikin ya tabbata da Musk ɗin ba. Kuma ba su so a mayar da dandalin Tiwita ya zama mallakin wani mutum mai zaman kansa ba. 

A wani jawabi da aka rawaito Musk ya yi a yayin amsar ragamar kamfanin, ya bayyana cewa ya sayi kamfanin ne don ƙara tabbatar da an ƙara samun ‘yancin fadar ra’ayi a shafin. Domin a cewar sa, ‘yancin fadar albarkacin baki ita ce ƙashin bayan tabbatar da Dimokuraɗiyya, kuma dandalin Tiwita a cewar sa, wata babbar kafa ce inda ake yin shawara a kan manyan abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan Adam da gobensa.

Da ma dai idan za a iya tunawa a makonni biyu  da suka gabata, attajirin Biloniyan ya sayi hannun jari mai tsoka sosai a kamfanin wanda ya kai Dalar Amurka $46.5, kafin daga bisani a wannnan makon ya saye kamfanin ɗungurugum. 

Shugaban Kwamitin mahukunta Tiwita, Bret Taylor ya bayyana cewa, sai da suka yi nazari a kan buƙatar Musk sosai kafin su kai ga amincewa ciniki ya faɗa. Kuma a cewar sa suna fata wannnan cinikin ya zama sanadiyyar ƙarin riba da kuma ƙarin arziki musamman ga masu ruwa da tsaki a kamfanin. 

 Sai dai akwai masu ra’ayin kada attajirin ya yi amfani da kafar sadarwar don yin kalaman sa na cika baki da musguna wa wasu ba kamar yadda ya ce manufarsa ta sayen kamfanin ba.