Ku kawo ƙarshen yajin aikin ASUU ko ku fuskanci bore – Gargaɗin Shugaban ɗalibai ga gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), Sunday Asefon ya bayyana cewa, ɗaliban Nijeriya sun shirya tsaf domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shiga.

Shugaban ɗaliban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 5 ga Mayu, 2022 yayin da ya ke magana a wani shirin gidan Talabijin na Channels mai suna ‘Sunrise Daily’.

A cewar Sunday Asefon, da alama gwamnati ba ta da niyyar kawo ƙarshen yajin aikin, ganin yadda aka karkata akalar zaɓe a shekarar 2023.

Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki bayan da ya yi wa gwamnatin tarayya barazanar cewa ba za a yi zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a Abuja ba har sai an warware matsalar yajin aikin ASUU.

ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu, saboda wasu matsaloli da ba a warware su ba, ɗaya daga cikinsu shi ne dagewar da ƙungiyar ta yi na yin amfani da tsarin bayyana gaskiya da riƙon amana na jami’ar (UTAS) a matsayin zavin biyan kuɗi, maimakon tsarin biyan albashi da ma’aikata na ‘Integrated Payroll and Personnel Information System’ (IPPIS).

A cikin wannan yajin aikin, Chris Ngige, Ministan Ƙwadago da Aiki, da Ƙaramin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, sun bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Asefon a lokacin da ya ke nuna rashin jin daɗinsa kan yadda gwamnatin ASUU ke tafiyar da yajin aikin ya ce, “muna maganar ilimi ne, maganar rayuwa muke yi,” inji shi.

“Shugabanni ba sa magana kan rayuwarmu, wazannan shugabannin da muka zaɓa; amma a yanzu hankalinsu fuskanci zaɓe. Wannan zaɓen da muke magana a kai shi ne saboda son zuciya da son rai.

“Idan ka samu damar ganawa da ASUU da Gwamnatin Tarayya, gwamnatin tarayya za ta ce maka sun tarar da matsala daga PDP, ita kuma ASUU za ta ce maka an yi wannan tattaunawar tun lokacin Jonathan, amma abin da muka yi imani a matsayinmu na ɗalibai shi ne gwamnatin yana cigaba; ya kamata su yi gyara tare da nemo mafita kan wannan lamari,” inji shi.

“Bai kamata mu kasance a ƙarshen kowane lokaci ba, don haka ya kamata su daina amfani da mu wajen yin siyasa”, inji shi.