Kwastom sun sake kashe wasu magidanta biyu da jikkata wasu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Motar jami’an kwastam da ke sintiri a babbar hanyar Katsina zuwa Jibiya ta hallaka wani magidanci a yayin da wasu mutane uku suka samu munanan raunuka. 

Lamarin ya faru ne jiya da misalin ƙarfe 3:00 na yamma bayan da magidancin ke tafiya a kan babur ɗinsa goye da fasinja, su kuma kwastam ɗin sun biyo wata mota ƙirar Peugeot da suke zargin masu fasa ƙwauri ne da ke safarar kayan abinci daga bakin iyaka zuwa cikin biranen ƙasar nan.

Yayar marigayin Ubaida Hashimu ta shaida wa Manhaja cewar motar ta niƙe ɗan uwan nata tare da fitar da wasu sassan jikin sa gami da ƙuna da ya samu a dukkan jikin sa bayan da motar ta ja shi a ƙasa ta yadda ba za a iya gane shi ba.

Marigayin yana da mata 2 da ‘ya’ya, yana kuma kan aikinsa na acava ne ibtila’in ya faru da shi kamar yadda Ubaida Hashimu ta shaida wa wakilin Manhaja a Katsina.

Haka zalika wasu mutane uku sun samu munanan raunuka bayan da motar da kwastam ɗin ke bi ta afka masu, inda ɗaya ya rasu bayan an kai shi asibiti, biyu kuma suna kwance a asibiti su na karvar magani.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Jibiya Hon. Bashir Sabi’u wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya bayyana aika-aikar ta jami’an kwastom dake aiki a shiyya ta biyu a matsayin rashin imani kuma abin da ba za a lamunta ba.

“Jami’an kwastam masu aiki a Zone B suna kashe mana mutane a Jibiya kamar kaji, suna cin mutuncin mutanen mu kamar mu ba ‘yan Nijeriya ba ne?, inji shi.

Hon. Sabi’u ya ce abin baƙin ciki sun leƙa motar da kwastom ɗin ke zargin ta masu fasa ƙwauri ce amma kuma ba su ga kayan komai ba.

Daga nan sai ya roƙi babban Sufeton ‘yan sandar ƙasar nan a kan ya kawo masu ɗaukin gaggawa.

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, Kwantarola na hukumar kwastam a jihar Katsina Dalha Wada Chedi ya bayyana cewar su na gudanar da bincike don sanin yadda lamarin ya faru.

Wannan ba shi ba ne karon farko da jami’an kwastam ke kashe al’ummar jihar waɗanda ba su ji ba su gani ba, ta yadda hatta Gwamnan jihar Aminu Bello Masari sai da ya maka su kotu ya kuma yi kakkausar suka akan yadda suke kashe masa al’ummar jiha, gami da haddasa munanan raunuka, sai dai ga alama har yanzu ba ta sauya zane ba.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya jami’an kwastam sun murƙushe wani mutum a kan hanyar Jibiya bayan da ya goyo buhun dusa a kan babur ɗinsa bayan sun yi zargin shinkafa ce ya ɗauko

Haka zalika a cikin watan Agusta, 2021 jami’an kwastam ɗin sun kashe mutane 10 suka kuma jikkata wasu 15 akan hanyar Jibiya a yayin da suke bin wani da su ke zargi mai fasa ƙauri ne.