Adamu ya kara wa’adin sayar da fom ɗin ’yan takarar shugaban ƙasa na APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ƙara wa’adin sayar da fom ɗin takararta a dukkan matakai yayin da ‘yan takara ke ƙara tururuwar sayen tikitin takarar shugaban ƙasa.

Tun farko an tsara kammala sayar da fama-faman ɗin a yau Juma’a, 6 ga watan Mayu, 2022.

Sai dai, cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa ya fitar ranar Laraba, jam’iyyar ta ƙara wa’adin zuwa ranar Talata, 10 ga Mayu.

A cewar wani sabon jadawali da Sakataren Tsare-Tsare na APC na Ƙasa, Sulaiman Muhammad Argungu ya fitar, an saka ranar 11 ga Mayu a matsayin ranar da dukkan ‘yan takara za su miƙa fama-faman da suka cike.

Yanzu za a gudanar da tarukan zaɓar wakilai wato daliget a dukkan ƙananan hukumomi na Nijeriya daga 12 zuwa 14 ga watan na Mayu.

Lamarin na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke ci gaba da samun ‘yan takara musamman na shugaban ƙasa, inda a Laraba Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole suka ƙaddamar da takarar tasu.

Kazalika, ana sa ran Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar zai ayyana tasa takarar a APC.