Jami’ar MAAUN ta naɗa Sheikh Muhammad Hassan a matsayin babban limamin Juma’arta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugabar Kwamitin Amintattu na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake Kano, Hajiya Dr. Maryam Sani Abacha ta buƙaci mahukuntan jami’ar da su naɗa Sheikh Muhammad Hassan a matsayin babban limamin masallacin Juma’a na jami’ar.

Sheikh Hassan shi ne limamin gidan Marigayi Janar Sani Abacha dake kan titin Gidado, Nassarawa GRA, Kano.

Buqatar naɗin Sheikh Hassan a matsayin babban limamin masallacin Juma’a na MAAUN na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan Talata 3 ga watan Mayu, 2022, mai ɗauke da sa hannun Maryam Abacha, kuma aka raba wa manema labarai a Abuja a ranar Laraba.

Dakta Maryam Abacha ta bayyana cewa a cikin wasiƙar, buƙatar ta ta taso ne bisa hujjar cewa Sheikh Hassan yana da ilimin addinin Musulunci da ake da buƙata da kuma cancantar gudanar da Sallah a masallacin duba da kasancewarsa mai haddar Alƙur’ani kuma amintacce.

A cewarta, Sheikh Hassan yana da ilimin da ake buƙata a fannin Fikihu, Shari’a da kuma iya harshen Larabci.

“Saboda haka muna so mu tabbatar wa duniya cewa Sheikh Muhammad Hassan shi ne babban limamin masallacin Juma’a na MAAUN Kano, muna taya shi murna da farin ciki tare da yi masa fatan shiriyar Allah,” in ji Maryam Abacha a cikin wasiƙar.

An haifi Sheikh Hassan a garin Gamborin Gala da ke jihar Borno a shekarar 1966. Ya kammala karatun Al’ƙur’ani a shekarar 1972, ya kuma kammala haddar Al’ƙur’ani a shekarar 1985.

Hakazalika a shekarar 1991 ya sake rubuta Al’ƙur’ani mai tsarki da hannunsa sannan a shekarar 2018 ya halarci taron manyan limamai na masallatan Juma’a a ƙasar Maroko.