2023: Ganduje na shirin nuna Inuwa Waya a matsayin ɗan takarar Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A daidai lokacin da zaven fidda gwani na ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC ke kusantowa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na ƙoƙarin fitar da ɗan takarar da yake sa rai zai gaje shi.

Tun dawowar dimukuraɗiyya a shekarar 1999, gwamnonin da suka kammala wa’adinsu na biyu suna lalubo waɗanda suke so su gaje su.

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 17 ga watan Mayu a matsayin ranar zaven fidda gwani na jam’iyyar ga masu neman takarar gwamna sai dai har yau Ganduje bai sanar da wanda yake so ya gaje shi ba.

Tun lokacin da mai ɗakin gwamnan, Hajiya Hafsat Ganduje ta yi nuni ga tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule Garo a matsayin wanda suke so ya gaje su, aka fara yaɗa jitar jitar cewa Ganduje na son goya wa Murtala Garo baya.

Sai dai wasu ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar ta APC rahotanni sun bayyana cewa suna shirin kin amincewa da wanda gwamnan zai nuna.

Wata majiya ta kusa da masu ruwa da tsaki kan batun ta shaida wa jaridar NIgerian Tracker cewa Gwamna Ganduje na son nuna Barista Inuwa Waya, yayin da zai sanya Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.

Wata majiya ta daban ta bayyana cewa tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano kuma mamba mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure ya shirya ficewa daga APC idan har Ganduje ya nuna Murtala Sule Garo da Barista Inuwa Waya a matsayin ‘yan takara.

Rahotanni sun bayyana cewa idan har masu ruwa da tsaki ba su amince da Inuwa Waya ba Gwamnan ka iya goyan bayan mataimakinsa Nasiru Gawuna tare da Murtala Sule Garo a matsayin Gwamna da mataimakinsa.

Sai dai majiyoyi da dama sun shaida cewa Gwamna Ganduje ya fi son nuna Inuwa Waya duba da kusancinsu amma yawancin shugabannin APC na qananan hukumomi 44 na goyan bayan Murtala Sule Garo.