Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Mai neman tsaya wa takarar kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen shekara ta 2023, Dokta Musa Babayo ya bayyana cewar, yana neman zama gwamna ne domin ya saka wa jiha bisa nauyi data ɗauka na karatun bokon sa tun daga makarantar firmare, sakandare, har ya zuwa jami’a.
Dokta Musa Babayo yace nauyin karatun sa tun daga ɗarnukan 60 zuwa 70 karamar hukumar en’e da Sarkin yanka ke jagoranci ne ta ɗauki nauyi, sa’annan gwamnatin jiha ta karɓa, yana mai cewar, karatun digirin sa ne na biyu ya samu tallafin ƙasar waje.
Babayo, wanda yake yin wannan jawabi yana tare da tawagar sa lokacin da ya ziyarci Sakatariyar Jam’iyyar APC ta jihar Bauchi, inda ya nuna sha’awar neman shiga takarar kujerar gwamna, ya kuma yi waiwaye da cewar, ya samu ilimin sa a matakin firamare da sakandare ne a garin Azare ta masarautar Katagum kafin ya zarce zuwa kwalejin BACAS dake garin Bauchi, daga bisani kuma zuwa Jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zariya, inda ya samu digirin sa na farko a fannin gudanar da mulki, ɓangaren ƙididdiga da lissafin kuɗaɗe.
Ɗan neman shiga takarar kujerar gwamnan wanda ya zaɓi sana’ar ayyukan banki, a shekarar 2008 ne Marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa ‘Yar’Adua ya naɗa shi shugaban Gidauniyar Tallafin Ilimi a matakin manyan makarantu da jami’o’i na tarayyar Nijeriya (TetFund) inda ya kyakkyawar rawar gani matuƙa gaya wajen bunƙasa ilimi a ɗaukacin faɗin ƙasar nan.
Ya yaba wa masarautar Bauchi da shiyyar kudancin jiha bisa tagomashi da suka yi wa masarautar Katagum na amincewa da fitowar gwamnan farar fula na farko, wato marigayi Abubakar Tatari Ali daga masarautar, yana mai cewar, tun daga wancan lokaci, zumuncin gudanar da aikin hukuma a tsakanin masarautun biyu, Bauchi da Katagum yake ta ƙarfafa.
Babayo, wanda yake riƙe da sarautar gargajiya ta Talban Katagum ya buƙaci shugabannin jam’iyyar APC da su yi jagoranci nagari tare da wanzar da adalci da nuna ya kamata yayin gudanar da ayyukan jam’iyya, su kuma guje wa nuna bambanci a tsakanin masu neman shiga takarar madafun mulki.
Talba ya shaida wa shugabannin jam’iyyar ta APC, “A matsayina na mai neman shiga takarar kujerar gwamnan jiha, Ina da ƙwarin gwiwar zaku gudanar da aiyukan ku babu son zuciya yadda za su kasance gamsassu wa mambobin jam’iyya. Saboda haka, ku gudanar da aiyukan jam’iyya iyakar iyawar ku, kuma Allah shine Alƙali.”
Babban tagomashi na ziyarar Talban zuwa sakatariyar jam’iyyar APC a Bauchi shine na miƙa wa jam’iyyar wani katafaren sabon ginannen ofishi domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan jam’iyya.
Da yake yin nasa jawabi, shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Alhaji Babayo Aliyu Misau ya tabbatar wa dan neman kujerar gwamnan cewa, jam’iyyar tasu zata sanya adalci, gaskiya da yakana a matsayin wani madubi na gudanar da ayyukan ta, ba tare da la’akari da inda mamba ya fito ba.
Alhaji Babayo Misau sai ya nemi haɗin kai da fahimtar mambobin jam’iyya, musamman Waɗanda suke da aniyyar shiga neman madafun mulki daban-daban, yana mai nuni da cewar, masu neman shiga takarar kujerar gwamna su kwana da sanin mutum ɗaya ne tak zai samu kujerar.
Misau ya ƙara bayar da tabbacin cewar, shugabannin jam’iyya za su yi iyakar iyawar su na tabbatar da ganin anyi adalci a tsakanin ‘ya’yan APC, haɗi da yin aiki da abinda ɗaukacin mambobi suka yi ittifaƙi, domin bi ko yin aiki da ƙa’idojin jam’iyya.
