2023: Ina fata a samu shugabannin da suka fi mu – Masari

*Ya buƙaci ’yan takara su cire gaba a tafiyar siyasa

Daga UMAR GARBA a Kataina

Duba da ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta a fannoni daban-daban, kama daga ɓangaren tsaro, tattalin arziƙi, ilimi da dai sauran ɓangororin da za su haɓaka cigaban Nijeriya, Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya yi fatan samun shugabanni waɗanda za su yi aiki fiye da su bayan kammala manyan zaɓukan da suke tafe na shekara ta 2023 lokacin da wa’adin mulkin zaɓaɓɓun masu riƙe da madafun ikon ƙasar ke ƙarewa.

Gwamna Masari ya bayyana cewar, ƙasar na buƙatar shugabannin da za su yi aiki tuƙuru a shekara ta 2023  fiye da abinda shugabannin da ke kan madafun iko a halin yanzu suka yi, domin shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Masari ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa manema labarai jim kaɗan bayan da ya kammala sallar idi a masallacin da ke Unguwar Modoji a fadar gwamnatin jihar.

“Nasarar wannan gwamnati shi ne, kawo shugabannin da za su yi aiki fiye da mu wannan shi zai sa mu ce ƙasarmu da jiharmu na cigaba. Mu na buƙatar shugabanni da za su yi aiki fiye da abinda mu ka yi a yanzu. Wannan shi zai sa ƙasar ta samu nasara,” inji shi.

A jawabin nasa albarkacin ranar Ƙaramar Sallah ya bayyana cewar, taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ɓarkewar annobar cutar Korona gami da matsalar rashin tsaro da kuma faɗuwar farashin man fetur sun shafi cigaban ƙasar matuƙa.

Masari ya jaddada cewar, akwai buƙatar masu kaɗa ƙuri’a su zaɓi shugabanni waɗanda za su himmatu wajen yin aiki, domin dawo da martabar ƙasar, don amfanin al’umma.

Daga ƙarshe ya yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya da haɓɓakar tattalin arziƙin Nijeriya.

A wani cigaban kuma, Gwamnan na Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya buƙaci masu neman tsaya wa takarar kujeru daban-daban a manyan zaɓukan da suke tafe na shekara ta 2023 da su kawar da gaba da ƙiyayya a tsakaninsu, saboda a cewarsa hakan zai iya halaka Nijeriya bakiɗaya.

Gwmana Masari ya yi wannan kira ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Ribas kuma mai neman takarar kujerar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Nyesom Wike, a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Katsina.

A cewar Gwamna Masari yin siyasa ba tare da gaba ba zai haifar da zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a ƙasar gabanin zaɓukan da suke tafe a shekarar 2023.

Masari ya kuma bayyana cewar fitowar mutane irin su Gwamna Wike, don neman tsaya wa takarar Shugaban Ƙasa alama ce da ta ke nuna cewar ƙasar a dunƙule ta ke ta yadda kowa zai iya neman shugabanci ba tare da fargabar ɓangaren da ya fito ba.

Tsohon gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Ɗankwambo, shi ne ke jagorantar tafiyar yaƙin neman zaɓen Gwamna Wike, wanda ya shaida wa Masari cewa, sun zo Katsina ne, don ganawa da wakilan jam’iyyar PDP na jihar, waɗanda za su halarci taron jam’iyyar na ƙasa, domin neman goyon bayansu.

Tun farko a wata sanarwa da Gwamna Wike ya fitar ta bakin mai taimaka masa akan yaɗa labarai, wato Kelvin Ebiri, ya bayyana cewar, “Ina son a hukumance na sanar da ku cewa Ina neman tsaya wa takarar Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, na kuma zo nan ne, don na gana da wakilan jam’iyya, waɗanda za su halarci babban taron jam’iyya a ranar 28 da 29 na wannan wata da muke ciki.”

Daga ƙarshe tawagar ta Gwmna Wike ta wuce zuwa Hedikwatar Jam’iyyar PDP ta Jihar Katsina, don ganawa da shugabannin jam’iyyar.