Jami’an tsaro sun yi ram da shugabannin PDP a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano sun cafke wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Kano. A yammacin ranar Larabar da ta gabata ne rikici ya ɓarke tsakanin shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Kano da wakilan hedikwatar jam’iyyar na ƙasa da za su wakilci babban taron jam’iyyar a jihar.

Rikicin ya afku ne a otal ɗin Tahir, inda ɗaya daga cikin wakilan hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa ya yada zango.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan rikicin an miƙa wasu shugabannin jam’iyyar na Jihar Kano guda biyu da suka haɗa da Ɗahiru Haruna da Idi Zare Rogo ga ofishin ‘yan sanda da ke Badawa.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Shehu Wada Sagagi, ya shaida wa manema labarai cewa, sun tarbi guda cikin wakilan jam’iyyar na ƙasa mai suna Barista Ekwudile a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, inda aka kai shi otel ɗin Tahir. Sai dai shi Ekwudile ya buƙaci masu masaukin da su kawo masa abin sha, inda suka fita domin kawo masa.

“Lokacin da suka dawo ɗauke da abin shan, kamar yadda ya buƙata, ba su tarar da shi a cikin ɗakin ba, amma daga baya sun gano shi a ɗaki mai lamba 811, wanda a nan ne rikici ya ɓarke,” inji shi.

Ya ce, duk da ya ke bai da tabbas kan musabbabin rikicin, amma dai ana iya danganta shi da mutanen da suka ga Ekwudile tare da su, inda a cewarsa wataƙila ya sa Ɗahiru Haruna da Idi Zare Rogo suka yi zargin cewa da akwai wata ƙullalliya.

Sai dai kuma wata majiya ta ruwaito cewa, tun a baya an samu ɓaraka a jam’iyyar PDP ta Kano, inda wasu ‘yan jam’iyyar ke biyayya ga tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Wali, wasu kuma ke da nasu shugabancin, amma hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa Shehu Wada Sagagi ta amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano.

Sagagi dai na ɗaya daga cikin masu biyayya ga tsagin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a baya-bayan nan ya fice daga jam’iyyar ya koma Jam’iyyar NNPP.