Rahoto

Nasko Ɗakingari da matasa 5,000 sun bar APC zuwa PDP a Kebbi

Nasko Ɗakingari da matasa 5,000 sun bar APC zuwa PDP a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Alhaji Nasiru Nasko Ɗakingari, tsohon ɗan takarar shugabancin Ƙaramar Hukumar Suru a ƙarƙashin Jam'iyyar APC kuma shugaban matasa daga ƙaramar hukumar, tare da matasa sama da 5,000 da ke goyon bayansa, sun bar Jam'iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP ta adawa a Jihar Kebbi. Da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Ɗakingari, Alhaji Nasko ya bayyana cewa, ana zaton adalci a APC, amma sai abin ya zama akasin haka wannan ainihi shi ne babban dalilin da ya sanya suka bar jam'iyyar. Ya ƙara da cewa tun da farko sun bayyanawa magoyabayan su da cewa bisa…
Read More
Mutanen ƙauyen Illela Babba, mai shekaru fiye da 200, na kukan rashin more dimukraɗiyya a Sakkwato

Mutanen ƙauyen Illela Babba, mai shekaru fiye da 200, na kukan rashin more dimukraɗiyya a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Al'ummar ƙauyen Illela Babba da ke a Ƙaramar Hukumar Mulkin Wamakko a Jihar Sakkwato na cigaba da nuna damuwarsu kan kasa shayar da su romon dimukuraɗiyya na samar masu da abubuwan more rayuwa, duk kuwa da irin gudunmawar da suke bayarwa na kai 'yan siyasa a madafun iko. Wakilin mu a Sakkwato, ya ziyarci ƙauyen na Illela Babba inda ya gane ma idonsa halin da mazauna ƙauyen ke ciki na rashin shayar da su romon dimokuraɗiyya, duk kuwa da cewa mulkin dimukuraɗiyya ake. Ga tsarabar da ya aiko mana: Hanyar shiga Illela Babba Tazarar ƙauyen…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da sabuwar hanyar Nguru-Gashua-Bayamari a Yobe

Buhari ya ƙaddamar da sabuwar hanyar Nguru-Gashua-Bayamari a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da buɗe sabuwar hanyar da Gwamnatin Tarayya ta kammala wadda ta tashi daga Nguru zuwa Gashua ta wuce Baymari tare da miƙa ta a hannun gwamnatin Jihar Yobe a ranar Lahadin makon jiya. Da yake jawabi a madadin Shugaba Buhari a wajen taron buɗe hanyar, Ministan Wutar Lantarki, Abubakar D. Aliyu, ya bayyana aikin hanyar a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da Gwamnatin Tarayya ta gudanar a faɗin qasar nan domin bunƙasa harkokin sufuri da tattalin arziki a ƙasar nan. Ya ce: “Kamar yadda za ku shaida, za…
Read More
An ƙaddamar da shirin KAZBO karo na uku

An ƙaddamar da shirin KAZBO karo na uku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato ta ƙaddamar shirinta na ƙarfafa mata iyayen marayu na kiyon kaji da aka fi sani da KAZBO wato kaza, zabo da mata ɗari da suka fito daga gundumomi daban-daban. Da yake jawabi lokacin ƙaddamar da shirin, Shugaban Zartarwar Hukumar ta Zakka da Waƙafi Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), ya ce manufar wannan shirin shine ƙarfafa uwayen marayu domin su iya dogaro da kansu ta hangar kiyon kajin. Ya bayyana cewa hukumar tasa ta samu ƙwarin guiwar ƙaddamar da wannan bisa nasarorin da aka samu tun fara shirin…
Read More
Ƙungiyar Ɗalibai ta BMGGG ta yi tir da yunƙurin assasa Dogara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa

Ƙungiyar Ɗalibai ta BMGGG ta yi tir da yunƙurin assasa Dogara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wasu gungun Musulmi dake ƙarƙashin lemar Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Nijeriya (MSSN) sun bayyana ƙarara cewar, ko da wasa ba za su taɓa goyon bayan yunƙurin da wasu ‘yan siyasa ke yi ba na ganin sun ɗora Yakubu Dogara a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa wa ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Asiwaju Ahmad Bola Tinubu a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC ba a gabanin babban zaɓen shekarar 2023. Gungun, da suke da laƙabin “Bauchi Muslim Good Governance Group (BMGGG)”, sun kuma ce, ba za su taɓa goyon bayan Dogara wa kowane irin muƙamin shugabanci na ƙasar…
Read More
Kwalejin Nasarawa za ta yi bikin cikar shugabarta shekaru biyu a kan kujera

Kwalejin Nasarawa za ta yi bikin cikar shugabarta shekaru biyu a kan kujera

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yanzu shire-shire ya yi nisa don gudanar da wani babban bikin cika shekaru biyu na shugabancin shugabar Kwalejin Kimiyya da Fasaha wato Mustapher Isah Agwai Polytechnic ta gwamnatin Jihar Nasarawa dake Lafiya babban birnin jihar, wato Misis Justina Kotso.  Shugaban sashin wasa labaran makarantan, Ali Hassan Mohammed ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake makarantar jiya Alhamis 30 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki.  Ya ce makarantar tana gudanar da babban bikin ne don murnar ɗimbin ayyukan cigaba da nasarori da shugabar makarantar,…
Read More
An ja kunnen tsofaffin sojoji su guji haɗa kai da ‘yan ta’adda

An ja kunnen tsofaffin sojoji su guji haɗa kai da ‘yan ta’adda

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya gargaɗi tsofaffin sojojin da suka yi ritaya su 125 daga rundunoni uku da ke ƙarƙashin runduna ta uku ta sojojin sulke da ke Jos, da su nisanci haɗa kai da 'yan ta'adda, da duk wasu masu neman kawo lalacewar tsaro a ƙasar nan, bayan sun koma kusa da iyalansu.  Babban Hafsan ya ce Rundunar Sojojin Nijeriya za ta cigaba da tuntuvar tsofaffin sojojin don amfani da shawarwarinsu da gudunmawarsu a ƙoƙarin da rundunar ke yi na yaƙi da ayyukan ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya. …
Read More
Yadda ’yan kasuwa suka mayar da titinan Zariya wurin kasuwanci

Yadda ’yan kasuwa suka mayar da titinan Zariya wurin kasuwanci

Daga MOH'D BELLO a Zariya Yanzu haka ƙananan 'yan kasuwa sun maida sababbin titituna da gwamnati jihar Kaduna ta kammala wajen kasuwanci a birnin Zariya dake ƙaramar Hukumar ta Zariya. Wakilinmu wanda ya leƙa kasuwar ya ruwaito cewa ƙananan 'yan kasuwar waɗanda da suka haɗu da masu sayar da kayan miya da ma’auna da mahauta har da masu sayar da man fetur a cikin galoli duk su ne suka mamaye sabo titin da ya tashi daga Ƙofar gidan Bellon Gima ya ratsa Kusfa zuwa Azaran Dabuwa da titin da ya tashi daga Ƙofar Gidan Bellon Gima zuwa Unguwar Ƙaura ta…
Read More
Aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 90 ne za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2023 – INEC

Aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 90 ne za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2023 – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce tana kyautata zaton aƙalla 'yan Nijeriya miliyan 90 za su kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen ƙasa mai zuwa na 2023. Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ofishin hafsan sojin saman Nijeriya IO Amao a Abuja babban birnin ƙasar. Shugaban hukumar zaɓen ya nemi taimakon rundunar sojan saman Nijeriya wajen ganin an isar da kayan zaɓe a ƙananan hukumomi a lokaci guda lokacin zaɓe. Yakubu ya ce aiki da rundunar shine mafita wajen kare yiwuwar samun tsaiko…
Read More
Ranar Yara: Ma’aikatar Mata ta sha alwashin samar da kyakkyawar Rayuwa ga Yara – Dr. Zahra’u

Ranar Yara: Ma’aikatar Mata ta sha alwashin samar da kyakkyawar Rayuwa ga Yara – Dr. Zahra’u

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A duk ranar 27 ga watan Mayun kowace shekara ne dai ake gabatar da ranar Yara ta Duniya wato World Children Day, taron na bana dai shi ne: “Samar da kyakkyawar makoma ga kowane Yaro”. Jihar Kano ma ba a barta a baya ba wajen aiwatar da wannan bikin, inda Gwamnatin jihar Kano tare da Ma’aikatar Mata da ci gaban al’umma ta gabatar a gidan Gwamnatin jihar, Kano. Tun da farko a jawabinta, Kwamishinar Mata da Cigaban Al’umma ta Jihar Kano, Dr. Zaharau Muhammad, ta bayyana muhimmancin wannan rana da kuma tasirin da ta ke…
Read More