Rahoto

Nasarawa 2023: Ko rikicin APC zai bai wa jam’iyyun adawa dama?

Nasarawa 2023: Ko rikicin APC zai bai wa jam’iyyun adawa dama?

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Kamar sauran jihohin ƙasar nan da ake sa ran gudanar da zaɓukan gwamnoni na shekarar 2023 dake tafe, a yanzu shirye-shirye da zirga-zirgar siyasa sun yi ƙamari a Jihar Nasarawa inda ‘yan takarar kujerar ta gwamnan jihar a duka jam’iyyu daban-daban ke cigaba da yin duka mai yuwa don tabbatar da sun yi nasarar lashe kujerar wadda a yanzu gwamnan jihar mai ci, Injiniya Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC ne ke zaune a kai.  Kamar dai yadda aka sani, Gwamna Abdullahi Sule wanda wa’adin mulkinsa zai qare ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023…
Read More
Masarautar Lafiya ta naɗa Dr. Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Nasarawa

Masarautar Lafiya ta naɗa Dr. Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A ƙarshen makon da ya gabata ne Masarautar Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa ta naɗa wa shugabar makarantar Kimiyya da Fasaha ta gwamnatin jihar wadda aka fi sani da Isa Mustapher Agwai Polytechnic dake Lafiya, Dokta Justina Kotso sarautar Tauraruwar Ilimin Matan Jihar Nasarawa.  Da yake jawabi jim kaɗan bayan ya naɗa wa shugabar makarantar sarautar, Mai martaba Sarkin Lafiya wanda shi ne kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiyan jihar, mai shari’a Sidi Bage mai ritaya ya bayyana cewa masarautar ta yanke shawarar naɗa wa Dokta Justina Kotso sarautar ne bayan ta yi la’akari da…
Read More
Magance matsalar tsaro ita ce kan gaba da zaɓen 2023, cewar Hashim

Magance matsalar tsaro ita ce kan gaba da zaɓen 2023, cewar Hashim

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon ɗan takarar neman shugabancin ƙasar nan, kuma jigo a Jam’iyyar APC dake jagorancin ƙasar nan, Mr. Gbenga Olawepo-Hashim ya roƙi shugabancin siyasar Nijeriya da kada su tara lissafe-lissafe da tunanin su kacokan akan zaɓen shekara ta 2023, a maimakon damuwar lamuran tsaro da suke da buqatar ɗaukar matakan gaggauwa, yana mai gargaɗin cewa: “Wajibi ne mu tabbatar da lafiyar zamantakewar jama’a, kafin waiwaitar lamuran gudanar da zaɓe, domin sai jama’a suna raye ne cikin kyakkyawan tsaro da ƙoshin lafiya sa’annan suke neman jefa ƙuri’ar zaɓe." Da yake gabatar da nasihar cewa, lamuran rashin tsaro…
Read More
Tsoffin ɗaliban Kwalejin Sa’adu Rimi na ‘yan ajin 92 sun yi taron cika shekara 30 da kammalawa

Tsoffin ɗaliban Kwalejin Sa’adu Rimi na ‘yan ajin 92 sun yi taron cika shekara 30 da kammalawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Tsofaffin ɗalibai na Kwalejin Ilimi ta Sa'adu Rimi da ke Kano Kano, 'yan ajin 1992 sun yi taron cika shekaru 30 da kammala makarantar. Taron wanda aka yi a ranar Lahadi a ɗakin taro dake harabar kwalejin ya samu halartar ɗimbin tsofaffin ɗaliban da wasu daga cikin malamai da suka koyar da su. Da yake bayani akan maƙasudin taron, shugaban riƙo na ƙungiyar, Mai Shari'a Kamilu mai Sikeli ya ce ƙungiyar ta samo asali ne daga gama makarantar saboda ba sa haɗuwa da juna sai in wani abu ya taso ko a ɗaurin aure ko…
Read More
Ina da burin ganin ana bada ilimi kyauta a Nijeriya – Ɗanburam

Ina da burin ganin ana bada ilimi kyauta a Nijeriya – Ɗanburam

Daga IBRAHIM A MUHAMMAD Ɗan takarar Majalisar Dattawa ta Kano ta Tsakiya a inuwar jam'iyyar PDP, Dakta Abubakar Nuhu Ɗanburan, ya bayyana cewa, ƙudurinsa shine, samar da abubuwan cigaba a Kano ta Tsakiya, domin duk abinda ya dami Jahar Kano ya tattara ne a Kano ta Tsakiya. Ya yi nuni da cewa, a Kano ta Tsakiya ne ake da mafi yawancin 'yan kasuwa da malamai da kusan dukka abubuwan da mutane ke buƙata suke so su yi na rayuwa. Don haka su yi abinda ya dace a wannan lokaci don tura wakilci da ya dace. Ya ce, ɗan Majalisar Dattawa…
Read More
Bikin yaye lauyoyi: Yadda rashin tsaro ya tilasta sauya wurin taro

Bikin yaye lauyoyi: Yadda rashin tsaro ya tilasta sauya wurin taro

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cigaba da taɓarɓarewar tsaro a babban birnin tarayya Abuja, ya tilasta wa ƙungiyar lauyoyin Nijeriya canja wurin taron yaye lauyoyin da suka kammala karatu zuwa Body of Benchers da ke Jabi a ranar 27 ga watan Yuli. A ranar Laraba ne makarantar koyon aikin shari’a ta Nijeriya ta yaye sabbin lauyoyi 1507 da aka kira zuwa aikin lauyoyi. An ƙaddamar da sabbin riguna a ɗakin taro na Body of Benchers da ke Jabi, Abuja a daidai harabar makarantar lauyan Nijeriya da ke Bwari. Darakta Janar na Makarantar Lauyoyin ya gode wa Hafsan Sojoji, Shugaban Sojoji,…
Read More
Bokayen da suka damfari wani ɗan siyasa Naira miliyan 24 sun faɗa komar EFCC

Bokayen da suka damfari wani ɗan siyasa Naira miliyan 24 sun faɗa komar EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani ɗan siyasa ya yi ƙarar bokansa da malamin tsubbunsa a wajen Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC) kan zargin damfararsa bayan ya faɗi zaɓen neman takara. Jami’an EFCC da ke Legas sun damƙe bokan da ɗan tsubbu, Alfa Abiodun Ibrahim da Wale Adifala ne, bisa zargin damfarar ɗan siyasar da yake neman kujerar Majalisar Wakilai a Jihar Ekiti da ba a bayyana sunansa ba Naira miliyan 24. Jaridar PM ta ruwaito cewa waɗanda ake zargin sun bugi hancin ɗan siyasar ne cewa za su yi masa aiki ya ci…
Read More
Aƙalla mutane miliyan uku za su shiga ƙangi kan shirin hana yanka jakuna a Nijeriya– Dillalai

Aƙalla mutane miliyan uku za su shiga ƙangi kan shirin hana yanka jakuna a Nijeriya– Dillalai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Dillalan Jakuna, DDA, ta ce shirin haramta yanka jakuna a ƙasar zai haifar da rasa ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya miliyan uku. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Ifeanyi Dike ne ya bayyana hakan a wajen wani taron kwana ɗaya da aka gudanar kan wasu ƙudirori takwas na ɓangaren noma. Taron jin ra’ayin jama’a wanda ya gudana a ranar Litinin ɗin da ta gabata, kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin noma da raya karkara a ƙarƙashin Sanata Bima Enagi ya jagoranta. Ƙudirin dai mai suna: “Ƙudirin tabbatar da dokar yanka jaki da fitar da…
Read More
Yadda jam’iyyar APC ke tangal-tangal a Kebbi

Yadda jam’iyyar APC ke tangal-tangal a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Tun bayan  tirka-tirkar zaɓen fid da gwanin yantakarar kujerar gwamna a jihar Kebbi Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta ɗauki hanyar rugujewa sanadiyyar rashin gaskiyar da mafi yawan 'ya'yan jam'iyyar ke ganin an tafka da kuma irin yadda salon mulkin da ake yi da ya saɓa wa hankali. Jihar Kebbi dai tana daga cikin jihohin da suka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ganin jam'iyyar APC ta kafa gwamnati  a dukkan matakai. Tun kama daga ƙananan hukumomi zuwa jiha, har tarayya a shekarar 2015, lokacin da iskar guguwar Buhari ta kaɗa. Duk da…
Read More
’Yan kasuwar Jihar Nasarawa sun bai wa Gwamna Sule lambar zaman lafiya

’Yan kasuwar Jihar Nasarawa sun bai wa Gwamna Sule lambar zaman lafiya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Jihar Nasarawa ta bai wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule wata lambar yabo ta musamman wato na tabbatar da zaman lafiya a jihar wadda ta kira 'Peace Award' a turance.  Da yake gabatar wa gwamnan lambar yabon a lokicin da ya jagoranci ɗimbin ‘ya’yan ƙungiyar don taya gwamnan murnar bikin sallar bana a gidan gwamnati dake Lafiya, babban birnin jihar, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar a jihar, Alhaji Musa Aliyu wanda aka fi sani da Turaki Gamji ya bayyana wa gwamnan cewa ƙungiyar ta yanke shawarar ziyartar shi ne tare da ba…
Read More