Magance matsalar tsaro ita ce kan gaba da zaɓen 2023, cewar Hashim

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon ɗan takarar neman shugabancin ƙasar nan, kuma jigo a Jam’iyyar APC dake jagorancin ƙasar nan, Mr. Gbenga Olawepo-Hashim ya roƙi shugabancin siyasar Nijeriya da kada su tara lissafe-lissafe da tunanin su kacokan akan zaɓen shekara ta 2023, a maimakon damuwar lamuran tsaro da suke da buqatar ɗaukar matakan gaggauwa, yana mai gargaɗin cewa:

“Wajibi ne mu tabbatar da lafiyar zamantakewar jama’a, kafin waiwaitar lamuran gudanar da zaɓe, domin sai jama’a suna raye ne cikin kyakkyawan tsaro da ƙoshin lafiya sa’annan suke neman jefa ƙuri’ar zaɓe.”

Da yake gabatar da nasihar cewa, lamuran rashin tsaro dake addabar sassan ƙasar nan sune abubuwan takaici fiye da lamuran zaɓe, Olawepo-Hashim, a cikin wani jawabi da jami’in sadarwarsa ya fitar, ya koka da cewar, fargabar rashin tsaro ya ta’azzari dukkan sassan ƙasar nan, kuma lamarin ya kai jallin Lahaula-Wala-ƙuwwata.

A kalaman Hashim: “’Yan ta’adda sun yi tunga a ƙofar shiga farfajiyarmu, ƙasar mu tana fustantar barazana, kazalika tsarin rayuwarmu, bambance-bambancen mu, dimukuraɗiyyar mu, zamantakewarmu, dukkansu sun shiga cikin hatsari. Lokaci yana ta yin nuni, kuma yana ƙurewa, dakarun sharri sun duƙufa ƙwace farfajiya ko helkwatar lmu.”

Bisa rahoton mashawarta, kamfanin dake sarrafa lamuran fasahar tsaro, fashi da harin ta’addanci, waɗanda suka addabi ɗaukacin ƙasar Nijeriya, da suka haddasa mutuwar mutane 7,222 da sace wasu mutane guda 3,823 a watanni bakwai da suka gabata.

Ƙididdigar ta’addancin a tsakanin shiyyuyi ya nuna cewar, a shiyyar Arewa maso Gabas, an samu aukuwa guda 777 waɗanda a cikinsu aka kashe mutane 2,052 da sace wasu guda 344. A shiyyar Arewa maso Yamma, an samu aukuwa guda 519 da suka haddasa mutuwar mutane guda 2,229 yayin da aka sace wasu guda 1,989.

Aukuwa guda 494 aka samu a shiyyar Arewa ta Tsakiya, inda aka kashe mutane guda1,748, kana aka sace wasu guda 950.

A cewar Olawepo-Hashim: “A shekaru biyu da suka gabata, mun yi magana akan matsalolin tsaro da suke addabar Nijeriya, muka kuma bayar da shawarwari akan yadda za a tinkare su, amma aka yi burus da dukkan shawarwarin mu.

“Yanzu lokaci ne da masu kishin ƙasa, taurarin mutane a cikin ayyukan gwamnati, da abokan ƙasar Nijeriya zasu yi cincirindo domin kare mutunci da kyawawan manufofin jumhuriyar mu, zamantakewar lafiya, zamanancewa da cigaban mu.

“Lokaci ɗaya wajabta da ƙasar mu za ta sake tsara fasalin yanayin tsaro ta yadda za a murƙushe duk wani fargaban rashin tsaro ɗungurungum, tare ta kawadda tushen ta’addanci da satar mutane domin neman kuɗin fansa a dukkan sassan ƙasar nan.”

Hashim ya ƙara da cewar, bisa lura da duk wani gungun ‘yan-ta’adda dake da tazarar tafiya cikin wa’adin awanni biyu zuwa Abuja (Karagar mulkin ƙasar nan) daga jihohin Neja da Kaduna, kada gwamnati ta wofintar da furucin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi akan yawaitar mayaqan ISWAP a ƙasar nan.

A watan Afrilu da ya gabata, ɗan takarar shugabancin ƙasar na shekara ta 2019 ya lura da cewar, tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu, gwamnati ta keɓe zunzurutun kuɗaɗe Naira tiriliyan 5.081 a sashin tsaro, tare da bayar wa a zahirance zunzurutun kuɗaɗe Naira tiriliyan 4.669 wa ma’aikatar tsaro daga shekarar 2016 zuwa yau, da kuma tsabar kuɗaɗe dalar Amurka biliyan ɗaya na sayen kayayyaki da na’urorin tsaro na soji, abin lura akan yaƙi da barazanar tsaro ko sunƙuranci shine, yana buƙatar tsararren martani da zai tunɓuke duk wani tushen fargaba.

“A halin da ake ciki yanzu, magana ce ta soki-burutsu ayi furucin cigaban rayuwa a cikin tarihi, yayin da gungun ‘yan-ta’adda suka yiwa helkwatar mu ƙofar rago, haɗi da nuna gazawar walwale ƙalubalolin tsaron mu. Duk da farmaki da sojoji suke yi domin kawar da fargaba a cikin dazuzzuka dake kewaye da helkwatar ƙasar nan, dabarbarun tsaro da suka yi wa helkwatar shinge duk suna kan idanuwan abokan gaba, kuma suna da kuzari, tanƙwara da dabarun kai hari wa kowane wuri a lokacin zaɓin su.”

Sai ya bayar da shawarar, “Kada mu yi sakacin karaya, yin jinkirin mayar da martani ga duk wata barazana ko ƙalubale wa ƙasar mu, kuma wajibi ne mu mayar da martani da ƙarfin zuciya gaba-gaɗi.”