‘Yan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan sandan Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja sun fara hai samame dazuzzuka da gine-ginen da babu kowa a cikin gari da unguwannin bayan gari.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Josephine Adeh ne ya faɗi hakan a ranar Laraba, kamar yadda kafar yaɗa labaran Channel ta ruwaito.

A yayin da take ƙaryata jita-jitar cewa akwai mafakar masu garkuwa da mutane a cikin Abuja, ta ce a kwanaki masu zuwa mazauna birnin za su ga an tsaurara matakan tsaro.

Harin ya zo ne ƙasa da sa’a 24 ba bayan da rundunar ‘yan sanda ta yi alƙawarin za ta fara tattara bayanan sirri da kuma kai samame da ɗaukar sauran matakan tsaro.

“A yau ‘yan sandan birnin tarayya sun fara kai hari dazuka da da gine-ginen da ba mutane a ciki a cikin gari da unguwannin bayan gari. Kuma yanzu muka fara,” inji mai magana da yawun ‘yan sanda.

“Mutane za su ga an tsarara tsaro a wurin shige da fice a birnin.”

Ya ƙara da cewa duk wanda aka kama za a tantance sa ɗauki bayanansu sannan a kai su kotu.