16
Dec
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Asabar 17 ga Disamba, 2022, za a gudanar da taron gangamin naɗin sarautar Alhaji Mustapha Usman Adamu Ka’oje a matsayin sarki na 13 a sarautar Bargu Ka'oje a fadar Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi. Wannan sanarwar ta fito ne daga fadar Sarkin Gwandu, Mai Martaba Alhaji Muhammad Iliyasu Bashar, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata. Tarihin rayuwar Alhaji Mustapha Usman Adamu Ka'oje: An haifi Alhaji Mustapha Usman Adamu Ka’oje a ranar 7 ga watan Maris, shekara 1976. Shi ne babban ɗan Mai Martaba Marigayi Alhaji Usman Adamu, Sarkin…
