18
Feb
*An bankaɗo Naira Tiriliyan 2.1 da aka ɓoye Daga AMINA YUSUF ALI Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana adadin yawan Nairorin da aka ɓoye waɗanda gwamnatinsa ta bankaɗo tun da CBN ya fara dokar canjin fasalin takardun Naira a Nijeriya. Sannan kuma ya roƙi 'yan Nijeriya a kan su zama masu haƙurin jure wahalhalun da dokar ta samar. A cewar Buhari, gwamnaninsa ta samu nasarar bankaɗo aƙalla Naira tiriliyan 2.1 aka ɓoye ba a bankuna ba. Tun daga lokacin da gwamnatin ta sanya dokar sauya fasalin kuɗi. Shugaban ƙasar ya yi wannan jawabi a ranar Alhamis ɗin 16 ga watan Fabrairu, 2023…
