02
Jun
Daga UMAR GARBA a Katsina Wata ƙasaitacciyar tawaga da ta ƙunshi gwamnoni masu ci da kuma tsofaffi, ta kai wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban-gajiya a mahaifarsa dake Daura ta Jihar Katsina a jiya Alhamis, 1 ga Yuni, 2023. Daga cikin gwamnonin akwai sabon gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, Dapo Abiodun na Jihar Ogun, Babajide Sanwo Olu na Jihar Legas, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Bala Muhammad na Jihar Bauchi, Hope Uzodinma na Jihar Imo da mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam. A sanarwar da ofishin babban mataimaki na musamman akan kafafen yaɗa labarai na zamani ya fitar,…
