Dalilin da ya sa al’ummar Gbagyi ke goyon bayan rantsar da Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Honorabul Cesnabmihilo Dorothy Nuhu-Aken’ova ta bayyana cewa ƙabilun Gbagyi na goyon bayan shirin rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu.

A cewar babbar kodinetan Ƙungiyar Magoya Bayan Bola Ahmed Tinubu a ranar Gbagyi wanda aka yi a Unity Fountain, wurin taron Tinubu Hangout da Ƙungiyar Goyon Bayan Tinubu (TSG) ta shirya a Abuja.

A cewarta, “A madadin ‘yan ƙabilar Gbagyi masu son zaman lafiya da karamci na Nijeriya da mazauna ƙasashen waje, da kuma ‘yan ƙabilar Gbagyi musamman mazauna Babban Birnin Tarayya, Ina taya zaɓaɓɓen Shugaban ƙasarmu maigirma, Bola Ahmed Tinubu da shi da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cikin tsafta da adalci.

“Mun kira wannan rana ta Gbagyi ne domin mu daƙile wannan labari tare da raba kanmu babu gaira babu dalili daga wasu miyagu da suka kai ƙara kotu suna iƙirarin wakiltar mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja a cikin ƙarar da suka yi domin dakatar da bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu,” ta ce.

Honorabul Dorothy Nuhu ta ce al’ummar Gbagy, waɗanda ke da yawan jama’a da ke karɓar baƙuncin mazauna Abuja sannan kuma su ne mazauna babban birnin tarayya Abuja, mun zo ne domin nuna goyon bayanmu ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da kuma gwamnati mai jiran gado.

Ta ce ’yan asalin Gbagyi da mazauna Babban Birnin Tarayya, mambobin da abokan Bola Ahmed Tinubu, muna buqatar mu sanya wa kanmu dabarun haɗin gwiwa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado da gwamnatinsa.

Har ila yau, mun zo ne don murƙushe labarin tare da raba kanmu ba tare da wata shakka ba daga wasu ’yan fashi da makami da suka kai ƙara kotu suna iƙirarin wakiltar mazauna babban birnin tarayya Abuja a cikin ƙarar dakatar da bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu.

‘Yar siyasar ta ce ta ba wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa tabbacin cewa za a gudanar da bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya da shugaban askarawar ƙasar a ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda aka tsara kuma maƙiya dimokraɗiyya za su ji kunya.

“Gwamnatinku tana samun cikakken goyon bayanmu da sauran ‘yan Nijeriya,” inji ta.

A nasa jawabin, Convener na Tinubu hangout, Mista Tosin Adeyanju ya ce, “Darakta Janar na Ƙungiyar Magoya Tinubu, Honorabul James Faleke ya umurci ni Tosin Adeyanju da in gudanar da taronsa domin nuna goyon baya ga nasarar da jagoranmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu, “za mu ci gaba da wannan taron na haɗin kai har zuwa jajibirin bikin miƙawa.”