Ba macen da za ta yi nasara babu namiji – Ayat Adamu

Daga AMINA YUSUF ALI

Hajiya Ayat Uba Adamu ta kasance shaharayyiyar ‘yar kasuwa ta intanet wacce ta jima tana gwagwarmaya kafin ta kai inda take a halin yanzu. Wakiliyar BLUEPRINT MANHAJA, Amina Yusuf Ali, ta samu zantawa da ‘yar kasuwar ta yanar gizo, kuma ɗaya daga cikin iyayen da suka kafa wata sabuwar ƙungiyar mata zalla masu kasuwancin intanet (WOVA). Sun tattauna akan rayuwarta, sana’arta, ƙungiya da sauransu. A sha karatu lafiya.

BLUEPRINT MANHAJA: Za mu so mu ji cikakken sunanki. 

AYAT UBA ADAMU: Bismillahirrahmanirrahim. Cikakken sunana shi ne, Hajiya Ayat uba Adamu.

Yi mana bayanin wacece Hajiya Ayat Uba Adamu?

Kamar yadda na faɗa a baya, sunana Ayat Uba Adamu, kuma an haifeni a jihar kano a unguwar Lamido cresent. Na yi makarantar Firamare da Sakandare a Kano, daga Nan na tafi Makarantar koyon aikin jinya ta jihar Kano na karanci difiloma a ɓangaren fasahar haɗa magunguna. Daga Nan nai shiga aikin gwamnati a shekarar 2005, a 2010 na shiga qilungiyar ƙwadago na rile muƙamai daban-daban har kawo yanzu. Yanzu da zama  ni ce sakatariya ta mata a haɗaɗɗadiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa reshen jihar Kano , wato MHWUN. Daga baya  na koma wa karatu a NOUN. Inda na karanci digirina a fannin public health. A yanzu haka ina aikin lafiya, kuma ina da aure da Yara 4. 

Bayan aikin gwamnati, ko akwai wata sana’a da kike yi? 

Eh, ina sai da kayan yara abinda ya shafi sutura, takalma, da ɗan abin kwalliya na yara , kusan dai duk abinda ya shafi Yara na ƙawa wato ado Ina saidawa. Amma ta yanar gizo, wato intanet. 

Yaushe kika fara kasuwancin yanar gizo?

Na fara kasuwancin intanet tun 2015 kamar wasa , a 2016 Allah Kuma Allah ya haxa ni da Dakta Bello galadanci na nemi ya siyo min takalmin yara  kasancewar yana zaune a Chana  na tura masa kuɗin (ni ce farkon wacce Dakta Bello Galadanci ya fara kasuwanci da ita, ni na fara ba shi kuɗina). Kuma duk ta intanet muka yi wanan ban san shi ba Kuma bai sanni ba. Cikin ƙasa da wata 4 na samu kayana Alhamdulillah. Daga nan aka fara har Allah ya kai mu yanzu.

Me ya sa kika zaɓi wannan nau’in kasuwancin na intanet? 

Na zaɓi kasuwancin intanet ne, saboda ni mai iyali ce, ga aiki, na zaɓe ta ne domin za ta fi min sauƙi da samun wadattacen lokacin aikina , karatuna, da ma iyalina.

To alhamdulillah, sai dai na gode wa Allah, don ya ba ni miji jajirtacce ma goya min baya a koyaushe. Yana taimaka min ta fannoni da dama. To wannan ya taimaka min ta fannin samun sauƙi a kasuwancina. Domin wasu lokutan ma, ko aikawa da kaya zan yi yakan taimaka ya kai min. Kuma yakan zauna min da yara wasu lokutan idan ina da aikin yamma. Sai ya kula da su har na dawo. Kuma sannan ni ma ina ƙoƙari na ga na sa mijina da gidana a farko a kan komai. Kuma mijina shi ne shugaba a kan komai. Samun da nake bai sa na nuna masa bai isa ba. Shi ya sa shi ma ba ya ƙyashi ko baƙin ciki. Saboda ba na shiga haƙƙinsa a kan sana’a ko aikina ba. Sannan ina tsare masa mutuncina dai-dai gwargwado. 

To sauran mata kuma fa da ba su samu jajirtaccen miji kamar naki ba, wacce shawara za ki ba su ko satar amsar yadda za su gwama aiki da kuma sana’a?

A gaskiya kasuwanci ko aiki ba zai tava yiwuwa ba, sai da goyon bayan namiji. Ba macen da isa ta yi su cikin nasara sai mijinta yana goyon baya, yana taimaka mata. Idan ba haka ba kuma, to ta haƙura. Su ma kuma matan da halinsu. Wasu lokutan mata ke sa wa a hana su aiki ko sana’a ko kuma namiji ya dinga ƙyashinsu. Saboda mata kan raina mazajensu daga zarar sun fara kama ƙasa. Shi kuma yana ganin a matsayinsa na shugaba ya kamata ki ba shi mutuncinsa. Haka wasu matan rashin kamun kansu na sa maza su hana su hulɗar kasuwanci ko ta aiki. 

Akwai rahoton kun buɗe wata ƙungiyar kasuwanci mai suna WOVA, mecece manufarta?

Ita dai ƙungiyar WOVA ta mata masu kasuwancin intanet ce. Kuma manufarta, haɗa kan mata masu wannan kasuwanci a yanar gizo domin samun aminci da kuma ƙara wa juna ilmin kasuwanci. 

Waye ya kafa WOVA, kuma a yaushe aka kafa ta?

WOVA tunani ne na mutum 6, wanda muka zauna muka dubi matsalolin da muke fuska a kan sana’ar, har Allah ya sa tunanin ya zo ɗaya, muka cimma Wannan buri. An kafa ta tun 2016, amma ba ta zama official ba, sai 2022 muka samu satifiket da duk abinda ake nema. Idan za a kafa ƙungiya  har Allah ya sa aka ƙaddamar da ita ran 13 ga Mayu, 2023 .

Kina ganin za a iya cimma manufar da ake bukata da ƙungiyar?

Ƙwarai kuwa , da taimakon Allah , da naku za a cimma wannan burin da manufar. Kusan zan ce ma an fara cimma manufar. Domin ko haɗa kan da muka yi muka samar da ƙungiyar ai har aka ji mu, aka gan mu, ai babbar nasara ce, domin yanzu, kaɗan daga matsalolin namu sun fara warwaruwa. Da ma ita matsala wuyarta a san ta , insha Allah idan an san ta to maganinta, ba zai wuyar samu ba, insha’Allah.

Wadanne nasarori kika samu a ɓangarenki?

Akwai Alhamdulillah, babbar nasara ita ce, na zauna da kowa lafiya a shafukan yanar gizo, wanda dalilin wannan na samu kasuwa mai albarka. Akwai mutanen da saboda sayen kaya muka zama kamar “Yan uwa. Sannan wata nasarar kuma ita ce daga shafin sada zumunta har na buɗe shago na zahiri Ina sai da kayan a ciki. Wanda Kuma ta dalilin kasuwanci ana zumunci dai-dai gwargwado da abinda Allah ya hore.

Waɗanne ƙalubale kuma kike fuskanta da harkokinki? 

Akwai ƙalubale da dama. Kaɗan daga ciki su ne, direbobi na ba mu ciwon kai, na  gida da na waje, akwai ƙararrawar tura kuɗi ta ƙarya, akwai rashin ilmin kasuwancin kansa ma.  

Meye burinkinki na rayuwa a nan gaba?

Kamar yadda muka  kafa WOVA Kuma yanzu duk kusan jihohin ƙasar akwai wakilai, muna fatan nan gaba kaɗan Allah wara sa mata albarka ta zagaye dukkan sauran jihohin har mu samu ofis a birnin tarayya wato Abuja. Sannan muna fatan a dalilin WOVA, mata su samu ilmin kasuwancin sosai yadda za su ƙara bunƙasa tattalin arzikinsu, da na jihohinsu, da ma ƙasa gabaɗaya. Wanda ko bayan ranmu, za a yi slfahari da abinda mu ka yi .

Akwai wanda ya ɗauki nauyin ƙungiyar? Kin san ƙungiya sai da kuɗi.

Babu Wanda ya ɗauki nauyinta, illah mu 6 ɗin nan da na faɗa miki. Sai tallafin mazajenmu, wanda da  taimakon Allah da nasu muka  kai har aka samu wannan nasara. Amma yanzu dai muna neman tallafi da shawarwari daga al’umma da ma ƙungiyoyi.

Ko akwai mutanen da suke samun wani abu a ƙarƙashin sana’arki?

Ƙwarai kuwa, akwai masu karɓar kayan su siyar su cire ribarsu, akwai yaran dake zaman shagon wanda su ma duk su biyun, akwai iyayensu a ƙarƙashinsu. Kin ga Alhamdulillah za mu ce, tunda ko a nan ka taimaki wani kai ma. 

Daga karshe, wanne kira za ki yi ga sauran mata waɗanda ba sa sana’a?

Ina kira gare su da su canja tunani, domin yawan roƙon miji yana dasashe ƙaunar mace a zuciyar maigida. Kuma an kai wani zamani da sai mu mata mun tallafa wa mazajenmu ko da kuwa da siyan gishiri ne. Domin yanzu rayuwar ta yi tsauri. In har mijinki ya samu ya sai miki kayan abinci, to ki gode Allah. Ke Kuma sai ki ɗora daga inda ya tsaya. Don haka, mata a dage da neman halal. Wannan sana’ar daga ɗakinki za ki yi ta , ba ruwanki da fita waje , babban daɗin kasuwancin intanet kenan ma.

Masha’Allah, muna godiya, Hajiya Ayat 

Ni ma na gode.