N-YED ta tallafa wa marayu da kayan masurufi a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

A ranar Lahadin da ta gabata ne ƙungiyar tallafa wa matasa da marayu da aka fi sani da N-YED ƙarƙashin jagorancin Kwamared Abdulsalam Haruna, ta gabatarwa da marayun dake gidan yara na Ƙaramar Hukumar Nasarawa Tallafin kayayyaki masu ɗumbin yawa dan tabbatar masu da irin gatan da suke da shi.

Da yake yi wa manema labarai jawabi yayin taron, Shugaban ƙungiyar na N-YED, Kwamared Abdulsalam Haruna, ya ce lokacin da ya fara tunanin kafa wannan ƙungiya bai tunanin za ta zama haka ba, ya ce duk abin da mutum ya sa niyya a rayuwarsa in dai mai kyau ne Allah zai taimake shi.

Kwamared ya ce wannan na ɗaya daga cikin aikin wannan ƙungiya na tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi, haka kuma idan aka taimakawa waɗannan marayu su ma za su ji tamkar suna da iyaye, ba a bar su a baya ba.

Shi ma Dr. Mustapha Muhammad da yake ɗaya daga cikin waɗanda suka gabatar da takarda yayin taron, ya ce lallai yana kara jinjina wa waɗannan matasa bisa ƙoƙarinsu na wannan aiki da suka haɗa da sauran muƙarrabansu.

Shugaban na ƙungiyar wanzar da dimuƙuradiyya da taimakon jama’a da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

“Kada mutum ya ce sai ya yi karatu zai zama mai ilimi a wannan lokaci zai kasancewa yana da ilimin kasuwanci da zai iya kawo ɗauki ga rayuwar jama’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, mafi yawan ƙasashen da suka cigaba ta fuskar ƙirƙira ba su kasance masu aiki da wani ilimi karatu ba sai dai na fasahar ƙirƙira, nan ma ya kamata a ce hakan yana faruwa a tsakanin irin wannan yara da za ka ga akwai masu basira amma kuma ba a bincikar hakan.

Daga ƙarshe, ya buƙaci al’ummar da su ƙara jin tsoron Allah wajen fitowa tare da zuba jarinsu ga irin wannan gida da kuma marayun da suke ganin ba su da gata, wannan zai taimaka matuƙa wajen kore duk wani haushi ko shakka ga marayun da aka taimaka mawa.

Wasu daga cikin kayan da ƙungiyar ta bada tallafin sun haɗar da sabulan wanka da wanki, bokitai, audugar mata, dabulan wanki kayan karatu kayan sawa da sauransu.