Rahoto

Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare ga nakasassu a jihar. Gwamnati ta ce nakasassu za su ci gajiyar shirin gwamnatin jihar na bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare muddin sun mallaki abubuwan da ake buƙata. Kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis. A cewar Kwamishinan, "Yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tabbatar da adalci da samun daidaiton samun ilimi ga kowane ɗan jihar, daidai da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa." "Tabbas za mu bada tallafin karatu ga waɗanda ke da…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta talauce lokacin da na karɓi mulki – Dauda

Gwamnatin Zamfara ta talauce lokacin da na karɓi mulki – Dauda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayyana cewa, ya tarar da jihar cikin wani mawuyancin hali a lokacin da ya karvi mulki. Lawal, wanda ya bayyana hakan a yammacin Larabar da ta gabata a wani taron tattaunawa da ƙwararru a Jihar Zamfara a Abuja, ya ce, jihar na cikin wani hali kyau a lokacin da ya karvi mulki. “Na yi imani da tarihin jiharmu, wannan shi ne karo na farko da ƙwararru da al’ummar jihar Zamfara ke zuwa don yin cuɗanya da juna. "Na yi farin cikin jin wasu maganganun da aka yi. Lallai abin…
Read More
Na san talakawan Nijeriya na shan wahalar cire tallafin fetur – Tinubu

Na san talakawan Nijeriya na shan wahalar cire tallafin fetur – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA aAbuja Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya fahimci irin wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur, yana mai tabbatar da cewa matakin na da amfani ga ƙasar nan, musamman wajen tabbatar da ci gaba a nan gaba. Tinubu, wanda ya karɓi baƙuncin tsoffin gwamnoni 18 da su ka yi gwamna tare a 1999, a fadar shugaban ƙasa, ya roki 'yan Nijeriya da su ƙara haƙuri. Ya kuma tabbatar wa 'yan ƙasa cewa ana shirin aiwatar da tsarin da zai magance raɗaɗin cire tallafin man fetur. Tinubu ya ce gwamnati za ta ƙara…
Read More
Tinubu zai tsayar da ranar ƙidaya a Nijeriya – Shugaban hukumar

Tinubu zai tsayar da ranar ƙidaya a Nijeriya – Shugaban hukumar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, ya bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu zai bayyana sabbin ranakun da Nijeriya za ta gudanar da ƙidayar jama'a da kuma gidaje. Shugaban NPC ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis bayan ganawarsa da shugaban ƙasar cewa ci gaba da gudanar da ƙidayar jama’a zai haifar da ƙarin kuɗaɗe. Kidayar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta tsara tun daga ranar 3 zuwa 7 ga watan Mayun 2023 an ɗage shi zuwa ranar da gwamnatin Tinubu ta tantance. Bayan ganawa da shugaban ƙasar a ranar Alhamis, Kwarra…
Read More
Kotu ta bayar da belin Abba Kyari bayan wata 18 a tsare

Kotu ta bayar da belin Abba Kyari bayan wata 18 a tsare

Daga MAHDI M. MUH’D Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bayar da belin tsohon shugaban ɓangaren ’yan sanda masu kai ɗaukin gaugawa (SARS), Malam Abba Kyari, bayan ya shafe watanni 18 a tsare. Kotun ta ce an bayar da belin ne kasancewar, dakataccen jami'in ɗan sandan bai tsere daga gidan yarin Kuje ba a lokacin da aka kai hari gidan yarin a ranar 5 ga Yuli, 2022. Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa, yadda Kyari da tawagarsa suka ƙi tserewa a lokacin da aka kai wa gidan yarin hari, inda kusan kashi 90 cikin…
Read More
INEC ta shigar da ƙarar kwamishinanta na Adamawa, Hudu Ari, a kotu

INEC ta shigar da ƙarar kwamishinanta na Adamawa, Hudu Ari, a kotu

Daga MAHDI M. MUH’D Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya (INEC) ta shigar da tuhume-tuhume shida a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, kan dakataccen kwamishinan zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sannun shugaban sashen wayar da kan al'umma na hukumar, Festus Okoye, ta ce an shigar da ƙarar ce a babbar kotun jiha da ke Yola, a Jihar Adamawa. Sanarwar ta kuma tabbatar da samun takardar kammala bincike kan laifukan da suka shafi zaɓe daga hannun ’yan sanda, bayan kammala bincike kan laifukan zaɓe da aka yi a babban…
Read More
Sabbin Hafsoshin Soja: Janar-Janar 103 na fuskantar ritaya

Sabbin Hafsoshin Soja: Janar-Janar 103 na fuskantar ritaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Baya ga shirin ritayar da ake shirin yi, za a kara wa jami’ai da dama ƙarin girma zuwa matsayi na gaba don cike guraben da manyan hafsoshin da suka yi ritaya za su samar a wani vangare na sake tsara ayyukan da sabbin shugabannin ma’aikata ke yi. Hakan dai na faruwa ne watanni shida bayan da manyan hafsoshin soja 24 da birgediya-janar 38 suka yi ritaya a watan Disambar da ta gabata bayan shafe shekaru 35 suna hidimar ƙasar. Tinubu ya sanar da murabus ɗin Janar Lucky Irabor wanda shi ne babban hafsan tsaron…
Read More
Tinubu ya sa hannu kan dokar tsawaita aikin alƙalai zuwa shekaru 70

Tinubu ya sa hannu kan dokar tsawaita aikin alƙalai zuwa shekaru 70

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattava hannu kan ƙudirin dokar da ke neman tsawaita wa’adin ritayar alkalan babbar kotun ƙasar daga shekaru 65 zuwa 70. Shugaban Ƙasa ya amince da ƙudirin dokar shekarun ritayar alƙalan Babbar Kotun ƙasar rana Alhamis, 8 ga Yuni, 2023. A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Abiodun Oladunjoye, Daraktan Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, ya ce Tinubu ya sanya hannu kan dokar “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Fifth Change) (No. 37), 2023,” wanda Majalisar Ƙasa ta 9 mai barin gado ta gabatar da shi.…
Read More
Nasarori da ƙalubalen da Ma’aikatar Jinƙai ta fuskanta a saƙon Minista Sadiya na bankwana 

Nasarori da ƙalubalen da Ma’aikatar Jinƙai ta fuskanta a saƙon Minista Sadiya na bankwana 

A wannan jawabi, za mu ji irin nasarorin da ma'aikatar jinƙai da kiyaye haɗurra (FMHADMSD) a ƙarƙashin Ministarta ta farko, Hajiya Sadiya Umar Farouq, a yayin da take bankwana da ma'aikatar.  A lokacin da shugaba Muhammad Buhari ya ƙirƙiri ma'aikatar jinƙai a ranar  21 ga Agusta, 2019, manufar ƙirƙirar tata a bayyane take wato, kawo ɗauki na jinƙai don ceto waxanda ibtila'i ya ritsa da su, talakawa, da kuma tsamo miliyoyin 'yan Nijeriya daga matsanancin talauci.   Shugaba Buhari ya zavi Sadiya Umar Farouq a matsayin ministar hukumar ta farko saboda irin rawar da ta taka a baya a matsayin kwamishiniyar…
Read More
Rundunar ’yan sandan Kano ta kama masu laifi 93 cikin mako guda

Rundunar ’yan sandan Kano ta kama masu laifi 93 cikin mako guda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama mutane 93 da ake zargi da laifuka daban-daban a cikin kasa da mako guda a jihar. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammed Usaini Gumel ne ya tabbatar da haka yayin ganawa da ’yan jaridu a ranar Laraba 31 ga watan Mayu. Gumel ya ƙara da cewa, binciken farko ya tabbatar da zargin da ake yi akan waɗanda aka kaman. Ya ce, daga cikin zarge-zargen da ake musu akwai kawo cikas da kuma ɗaukar nauyinsu da aka yi don su kawo tarnaƙi yayin bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnati ta…
Read More