Buhari ya bai wa Tinubu lambar girmamawa mafi daraja ta Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Muhammmadu Buhari ya bai Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, lambar girma mafi daraja ta ƙasar wato ‘Grand Commander of the Order of the Federal Republic’ (GCFR).

Hakazalika, Buharin ya bai wa mataimakin shugaban ƙasar mai jiran-gado, Kashim Shettima lambar girmamar ta biyu a daraja wato GCON ‘Grand Commander of the Order of Niger’.

Shugaban ya ba su lambobin da kuma takardun mulki ne a Abuja, a shirye-shiryen da ake yi na rantsar da sabuwar gwamnati, ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu, bayan kammala wa’adinsa na biyu na shekara huɗu-huɗu.

Za a rantsar da sabuwar gwamnatin ne bayan zaɓen 2023, wanda ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu ya yi nasara.

Sai dai kuma Atiku Abubakar na PDP wanda ya zo na biyu da Peter Obi na jam’iyyar Labour wanda ya zo na uku tare da jam’iyyunsu suna ƙalubalantar nasarar a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *