Hajjin Bana: Gwamnati za ta fara jigilar maniyyatan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, ta bayyana cewar ta kammala shirye-shiryen fara jigilar maniyyata na shekarar 2023 daga jihar zuwa ƙasa mai tsarki.

Babban Daraktan hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ne ya sanar da hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a ɗakin taronta, da ke kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Malam Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina.

Ya ce a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 hukumar za ta fara jigilar maniyyatan jihar.

Kuki ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki waɗanda suka nuna sadaukarwa don ganin aikin Hajji na shekarar da ta gabata ya samu nasara, daga nan sai ya buƙace su a kan su ɗora da irin wannan jajircewa don ganin an samu nasarar aikin Hajjin bana.

Da yake jawabi, wakilin Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, da ke shiyyar Kano, Bashir Lawal Dutsinma, ya ce jirgin farko na maniyyatan bana zai tashi ne da alhazan jihar Nasarawa a ranar 25 ga watan Mayu, 2023.

A jawabai daban-daban da wakilan kamfanin Max Air, hukumar shige da fice, hukumar fasa ƙwauri, ‘yan sanda da dai sauransu duk sun bayyana kayakkyawan shirin da suka yi don tunkarar aikin Hajji na bana.

Haka zalika, mai magana da yawun hukumar alhazai ta jihar Katsina, Badaru Bello Karofi, cikin wata sanarwa ya bayyana cewar hukumar ta raba wa maniyyatan jihar jakukkunan hannu da kuma sutura ta bai-ɗaya.