Tsaro, lafiya, noma da sufuri sun samu kaso mafi rinjaye a kasafin 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Nijeirya ta ƙara ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2023 daga Naira tiriliyan 20.51 zuwa 21.82 sannan ta amince da shi.

Kwamitocin kasafin kuɗi na Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun ce ƙarin Naira tiriliyan 1.3 na kasafin kuɗin ya biyo bayan ƙarin kuɗaɗen da aka ware wa hukumar ƙidaya ta ƙasa gabanin ƙidayar jama’a a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 173 da aka ware wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, gabanin babban zaɓen 2023.

Rundunar sojojin Nijeriya da rundunar ‘yan sandan Nijeriya, da ma’aikatun noma, lafiya, jiragen sama, da kimiyya da fasaha suma sun samu ƙarin kaso.

Majalisar Dokokin Ƙasar ta kuma ƙara ma’auni na farashin man fetur da aka tsara na kasafin kuɗin daga dala 70 zuwa dala 75 kan kowacce ganga.

Sai dai majalisar ta ci gaba da riƙe wasu ma’auni kamar yadda shugaban ƙasa ya gabatar a baya kamar gangunan mai miliyan 1.69 a kowace rana, Naira 435.57 zuwa dalar Amurka; Kashi 3.75 cikin 100 na ci gaba da kaso 17.16 cikin 100 na hauhawar farashin kayayyaki.

Da ya ke gabatar da rahoton a zauren Majalisar Dattawa, shugaban kwamitin kasafin kuɗi, Sanata Barau Jibrin (APC Kano ta Arewa) ya ce, daga cikin kasafin Naira tiriliyan 21.827, Naira biliyan 967.486 na kuɗin ba bisa ƙa’ida yake ba.

A ƙarƙashin Naira tiriliyan 967.48 na kuɗaɗen da doka ta tanada, ofishin Majalisar Dokokin ƙasar yana da Naira biliyan 30.492; Majalisar Dattawa ta samu 33.267; Majalisar Wakilai, N51.994bn; Hukumar Hidima ta Majalisar, 10.555; mataimakan majalisa, 16.520; ayyukan gama-gari 11.307; Cibiyar Nazarin Majalisu da Dimokuraɗiyya ta Ƙasa, 7.411.

Sauran sun haɗa da: Naira biliyan 30.173 na sallama da ƙaddamar da ‘yan majalisa na 9 da 10 masu fita da masu shiga; N10 don gina ginin NASC; 2.5 don kammala hedikwatar NILDS da dai sauransu.

A wajen majalisar ƙasa, an ware naira biliyan 165 ga majalisar shari’a ta ƙasa, N119.9 na hukumar raya yankin Neja-Delta da kuma naira biliyan 103 na ilimi na bai ɗaya.

A cikin kasafin Naira tiriliyan 5.972 da ake shirin kashewa, Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta samu biliyan N398.275, sai kuma ma’aikatar tsaro N285.045bn, Ma’aikatar Noma da Raya Karkara biliyan N248.358, Ma’aikatar Ilimi, Naira biliyan 153.735bn.

Sauran sun haɗa da Ma’aikatar Lafiya, Naira biliyan 134.909bn, Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, N132.572bn; Ma’aikatar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare na Ƙasa, biliyan N166 747bn; Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Naira biliyan 70.331; Shugaban Ƙasa, Naiea biliyan 20.115bn; Ma’aikatar Cikin Gida biliyan N45.622; Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya biliyan N83.256 da dai sauransu.

Bayan zartar da kasafin kuɗin shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya amince da shi kafin shekarar ta ƙare domin ci gaba da aiwatar da tsarin kasafin kuɗi na watan Janairu zuwa Disamba.

A halin da ake ciki kuma, Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta amince da ƙarin kasafin kuɗi Naira biliyan 819.54 da gwamnatin Buhari ta nema.

A cewar shugaban, ƙarin kasafin na nufin taimakawa wajen gyara ababen more rayuwa da ambaliyar ruwa ta lalata a faɗin ƙasar.

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya nemi amincewar majalisar dokokin ƙasar kan ƙarin kasafin kuɗi na Naira biliyan 819.54.

Don haka Majalisar Dattawan ta ba da buƙatar yin la’akari cikin gaggawa tare da zartar da ita ta hanyar zartar da tsarin da ake buƙata a cikin mintuna 30.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce, ƙarin wa’adin zai samar da lokacin da ake buƙata don aiwatar da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 819.5 na 2022 da shugaban ƙasa ya gabatar.

Sai dai Sanata Muhammad Ndume (APC Borno ta Kudu), a yayin wata ’yar gajeruwar muhawara kan buƙatar, ya ce ba zai yiwu ba a fara aiwatar da ƙarin kasafin kafin watan Maris na 2023 ba.