An ja kunnen tsofaffin sojoji su guji haɗa kai da ‘yan ta’adda

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya gargaɗi tsofaffin sojojin da suka yi ritaya su 125 daga rundunoni uku da ke ƙarƙashin runduna ta uku ta sojojin sulke da ke Jos, da su nisanci haɗa kai da ‘yan ta’adda, da duk wasu masu neman kawo lalacewar tsaro a ƙasar nan, bayan sun koma kusa da iyalansu. 

Babban Hafsan ya ce Rundunar Sojojin Nijeriya za ta cigaba da tuntuvar tsofaffin sojojin don amfani da shawarwarinsu da gudunmawarsu a ƙoƙarin da rundunar ke yi na yaƙi da ayyukan ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya. 

Ya bayyana haka ne cikin saƙon da ya aike wajen taron liyafar bankwana da aka shiryawa wasu manyan jami’an soja su 10 da ƙananan jami’ai masu muƙamai daban-daban su 125 da suka ajiye kakin soja cikin shekarar da ta gabata ta 2021. 

Ya ce, rundunar sojojin Nijeriya za ta cigaba da mayar da hankali wajen kula da walwalar manya da ƙananan jami’an ta da ke bakin aiki da waɗanda suka yi ritaya, domin yabawa da irin gudunmawar da suka bayar da wacce suke kan cigaba da bayarwa.