Daga JOHN D. WADA a Lafiya
A yanzu shire-shire ya yi nisa don gudanar da wani babban bikin cika shekaru biyu na shugabancin shugabar Kwalejin Kimiyya da Fasaha wato Mustapher Isah Agwai Polytechnic ta gwamnatin Jihar Nasarawa dake Lafiya babban birnin jihar, wato Misis Justina Kotso.
Shugaban sashin wasa labaran makarantan, Ali Hassan Mohammed ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake makarantar jiya Alhamis 30 ga watan Yunin shekarar 2022 da ake ciki.
Ya ce makarantar tana gudanar da babban bikin ne don murnar ɗimbin ayyukan cigaba da nasarori da shugabar makarantar, Misis Kotso ta cimma tunda ta hau kujerar shugabancin makarantar kawo yanzu.
Ali Hassan Mohammed ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa kawo yanzu cikin shekaru 2 kacal da ta yi a matsayin shugabar makarantar, Misis Justina Kotso ta kawo canje-canje da dama tare da ƙirƙiro da kuma aiwatar da wasu muhimman ayyukan cigaba a makarantar da suka haɗa da sabon tsarin biyan kuɗaɗen makarantar da ake kira Student Payment Portal a turance da kafa na’urorin wutar lantarki a harabar makarantan da canja itatuwan wutar lantarkin daga na itace zuwa na kankare da ɗaukar ma’aikata da dama waɗanda ke koyarwa dama waɗanda ba sa koyarwa da fara ginin ɗakunan kwanan ɗaliban makarantar da ginin sabon babban ɗakin karatu na makarantar da dai sauransu.
Har ila yau a cewar mai magana da yawun makarantan Ali Hassan Mohammed ya ce akwai kyakkyawan dangantaka tsakanin makarantar da gwamnatin jihar, inda sau da yawa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ke yaba wa Misis Justina Kotso dangane da namijin ƙoƙari da take yi wajen ɗaukaka martabar makarantar.
Daga nan sai ya yi amfani da damar inda ya buƙaci malamai da ɗaliban makarantan baki ɗaya su cigaba da bai wa mahukuntan makarantar cikakken goyon baya don basu damar cigaba da samar musu da ingantaccen ilimi daidai da zamani, su kuma fito da yawansu su taya Misis Justina Kotso murnar bikin na cikanta shekaru 2 a kujerar shugabancin makarantan wadda a cewarsa ana sa ran za a gudanar a watan Yulin nan na shekarar 2022.