Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Wasu gungun Musulmi dake ƙarƙashin lemar Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Nijeriya (MSSN) sun bayyana ƙarara cewar, ko da wasa ba za su taɓa goyon bayan yunƙurin da wasu ‘yan siyasa ke yi ba na ganin sun ɗora Yakubu Dogara a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa wa ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Asiwaju Ahmad Bola Tinubu a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC ba a gabanin babban zaɓen shekarar 2023.
Gungun, da suke da laƙabin “Bauchi Muslim Good Governance Group (BMGGG)”, sun kuma ce, ba za su taɓa goyon bayan Dogara wa kowane irin muƙamin shugabanci na ƙasar nan ba, suna mai faɗin, “idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira, mun dai shaida maku matsayar mu, da fatar waɗanda suka ga tasirin hakan, za su yi yaƙinin wannan madogara tamu”.
Gungun Musulmin, a wani taron manema labarai a garin Bauchi a ranar Lahadi da ta gabata sun ce, sun yi mamakin yadda wasu Musulmi, musamman daga Arewacin ƙasar nan suke ta kai gwauro da marin nuna Yakubu Dogara a matsayin mutum nagari, suna masu bayyana cewar, duk yadda ƙoƙarin kwarzanta Dogara da kwalliyar cewa shi mutum ne na kowa, wannan gungun suna ganin lamarin ba haka yake ba.
Sun yi tababar cewa: “Mu da ke wannan gungu, muna buƙatar ganin Dogara ya kawo ko ya yi yunƙurin kawo wata maslaha da za ta share wani fage da Musulmi waɗanda aka kore su daga garinsu na iyaye da kakani, wato Tafawa Ɓalewa su koma matsugunin su na asali, ko kuma a kakkafa masu rumfuna na zaman wucin gadi a cikin gonakinsu dake kewaye da garin Tafawa Balewa da aka ƙwace masu a cikin rikici ko tashin-tashina da aka yi a shekarun baya.
BMGGG ta kuma lura da cewar, Musulmi da yawa sun ɗauki Dogara Yakubu a matsayin wani mutumin kirki ne mai karimci da yake yin cuɗanya da kowa da kowa, ta ce wannan dodorido ne da wasu mutane ƙalilan na bayan fage suke hasashe, amma ba tarin jama’ar Musulmi ba daga mazaɓarsa ko ɗaukacin Jihar Bauchi.
“Akwai hujjoji masu yawa akan halayyarsa dagane da yadda yake azabtar da jama’ar Musulmi, musamman waɗanda suke cikin mazaɓarsa ta Dass/Tafawa Ɓalewa/Bogoro a dukkan lamura da suka jiɓanci shugabanci da fannin ilimi, domin nakasa cigabansu ko ƙarfafa su yadda za su zauna akan ƙafafunsu, domin su yi kan-kan-kan da jama’ar ƙabilarsa.
Waɗannan gungun Musulmi a wata ganawa da manema labarai a garin Bauchi a ranar Litinin data gabata a ƙarƙashin jagorancin shugaban su, Barista Khalil Abdullahi, wanda yake tuhumar Dogara akan waɗanne dalilai suka sanya yake wawure duk wata dama da ta kasance ta ɗaukacin jama’ar Bauchi ne wa mutanen ƙabilarsa a zamanin da yake kakakin majalisa, har ma zuwa yau, yana cewa, suna da hujjoji da alƙaluma masu yawa na yadda ake ci da gumin Musulmi, har ma da fifita waɗanda ba ma ‘yan Jihar Bauchi ba ne.
Barista Khalil Abdullahi ya ce sun daɗe suna mamakin yadda Jihar Bauchi da take da ƙananan hukumomi guda 20, amma Dogara ba ruwansa da ƙarfafa jama’ar wata hukuma face hukumar data tara ƙabilarsa.
Gungun ta BMGGG ta ce tana ɗauke da hujjoji na yadda Dogara ko sau ɗaya bai taɓa jajanta wa Musulmi ba a dukkan rikice-rikicen da aka yi a baya a garin Tafawa Balewa wanda ya fara tun daga shekara ta 1991, kuma bai damu da ya san halin da Musulmi a cikin mazaɓarsa suke ciki ba duk da sanin rikice-rikicen addini ko ƙabilanci da aka yi ba a baya shekaru aru-aru.
Abdullahi sai ya ƙalubalanci ‘yan kanzagin Dogara da sune neman cusa shi cikin miliyoyin zukatun jama’ar Arewacin ƙasar nan, da cewar, idan gaskiya suke faɗi, me ya gaza su tsayar da shi ɗan takarar neman kujerar sanata a Bauchi ta Kudu, ko kuma mataimakin gwamna wa ɗantakara Marshal Sadiq Abubakar, kafin su nuna shi a matsayin mutumin da zai yi wa Tinubu mai neman shugabancin ƙasar nan.
Suka kuma ce gazawar Dogara ya kafa wata kwamiti da zai sulhunta Musulmi da Kiristocin dake zaune a cikin Ƙaramar Hukumar Tafawa Ɓalewa ita ma wata illar ce da ke nuna cewar, Dogara ba zai iya shugabantar jama’a da adalci ba.
