’Yan daba sun far wa ’yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne wasu ɓatagari su ka kai wa ‘yan majalisar dokokin Jihar Bauchi farmaki a gidan shaƙatawarsu, inda su ka raunata mutum shida tare da lalata motoci da tagogi a gidan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, (NAN) ya bayar da rahoton cewa majalisar ta faɗa cikin rikicin shugabanci inda a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne mambobi 22 su ka kaɗa ƙuri’ar rashin goyon baya ga shugaban majalisar, Abubakar Suleiman da sauran masu riƙe da muƙamai a majalisar.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Babale Abubakar, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin a Bauchi cewa, harin da ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma, a daidai lokacin da ‘yan majalisar ke gudanar da taro, ya yi sanadin jikkata shida daga cikinsu.

“Aƙalla motoci shida maharan suka lalata tare da farfasa gilashin tagogi.
“Sun fi 100 kuma suna ɗauke da bindigogi, kokara da adduna,” inji shi.

Ya cigaba da cewa: “Abin ban tsoro ne, wasu daga cikinmu sun gudu zuwa ƙofar fita kuma sun ji rauni sosai,” inji shugaban masu rinjaye.

“Al’amari ne mai ban tsoro. Abin bakin ciki ne,” inji shi.

By Editor