Rahoto

Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako, sannunku da jimirin bibiyar jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan makon, za mu tattauna kan darasin da a wannan zamani ya fi ci wa mata tuwo a ƙwarya tsayin lokaci, musamman ma a ƙasar Hausa. kafin mukai ga tattauna ƙorafin mata kan rashin ciyar da su da mazansu ke yi, bari mu fara kan mazan wanda wataƙila mu samo wata mafita ko fahimta a cikin lamarin. Akwai wani lokaci can bayan a kafar sadarwa ta ɗ wanda a baya aka fi sani da…
Read More
Abu ne mai muhimmanci haɗa kai domin bunƙasa cigaban al’ummar Rano – Sarkin Rano

Abu ne mai muhimmanci haɗa kai domin bunƙasa cigaban al’ummar Rano – Sarkin Rano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isah Umaru ya yi kira ga 'yan asalin ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure akan su cigaba da haɗa kansu da tafiya tare domin  bunƙasa cigaban al'ummar yankin. Ya bayyana haka ne a yayin taron karrama 'yan asalin Rano dake ayyuka daban-daban a faɗin  ƙasar nan da aka yi a garin Rano  ranar Asabar. Ya kuma ja hankalin mutanen da aka karrama su buɗe wata ƙungiya ta daban su haɗa kai da ƙungiyar RAKIBU da za su riƙa fito da al'amuran da zai taimaka ga cigaban al'ummar masarautar Rano.…
Read More
Dandalin shawara: Mahaifina ya ce ba zan yi aure ba har sai na mallaki gida na kaina

Dandalin shawara: Mahaifina ya ce ba zan yi aure ba har sai na mallaki gida na kaina

Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Assalamu alaikum. 'Yar'uwa barka da wannan lokaci. Ya iyali. Sannu da ƙoƙari. Don Allah shawara nake nema kan matsala ta. Wallahi na yi karatu har na kammala digiri na farko, na yi bautar ƙasa har yanzu na kai na samu aiki a ƙaramar hukuma, kusan shekara ɗaya da rabi kenan. To shi ne na yi ɗan tanadi da ɗan abinda nake samu na albashi zuwa 'yar buga-buga da nake yi na haɗa lefe, na tanadi kuɗi har dubu ɗari, sannan na je ga mahaifina kan sha’anin nema min aure. Anan fa ya ce bai san da…
Read More
Motsa jiki ma kwalliya ne

Motsa jiki ma kwalliya ne

Daga AISHA ASAS Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne. Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaƙulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan…
Read More
Ka kuwa san muhimmancin lokaci?

Ka kuwa san muhimmancin lokaci?

Dag BILKISU YUSUF ALI Ka taɓa jin kamar kwanakin ka suna tafiya cikin sauri, amma kai ba ka cimma komai ba? Wannan shi ne alamar rashin amfani da lokaci yadda ya kamata matsalar da take shafar miliyoyin mutane a duniya, tana jawo damuwa, rashin nasara, da wahalhalu marar misaltuwa. Lokaci shi ne mafi mahimmancin albarkatun da ɗan Adam ya ke da shi. Kowa na da sa’a 24 a rana, amma yadda mutum ke amfani da wannan lokaci shi ke bambanta tsakanin nasara da rashin nasara a rayuwa. Lokaci abu ne mai tafiya ba tare da dakatawa ba. Ba za a…
Read More
Jerin mutanen da suka taka rawar gani wajen samun ’yancin kai a Nijeriya

Jerin mutanen da suka taka rawar gani wajen samun ’yancin kai a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da Nijeriya ke cika shekaru 65 da samun ’yancin kai, Jaridar Blueprint Manahaja ta yi bincike daga wurare daban-daban dangane da mutanen da suka fi taka rawa wajen fafutukar nema wa Nijeriya ’yanci. Za mu tattaro mutum bakwai waɗanda suka yi fice wajen samun ’yancin: 1. Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto (Yuni 12, 1910 - Janairu 15, 1966): An haifi Sir Ahmadu Bello a garin Rabbah na jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya. Sardauna na daya daga cikin jagororin Nijeriya da suka yi fice a duniya. Ahmadu Bello ya riƙe sarautar Sardaunan Sokoto kuma ya…
Read More
Gwamnatin Tinubu na dukan ‘yan Nijeriya da ɗanyen kara – Mustapha Tinubu 

Gwamnatin Tinubu na dukan ‘yan Nijeriya da ɗanyen kara – Mustapha Tinubu 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da cewa mutum ne mai son cigaban al'umma  amma sai dai ba shi da mashawarta a gwamnatinsa masu kishi, da a ce akwai irinsu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso jagoran Kwankwasiyya a kusa da shi da talaka ya yi sambarka saboda zai kawo gyara. Hon. Mustapha Muhammad Tinubu (Chiranchi) jigo a tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai bayan ɗaurin aure da aka yi na 'ya'yansa. Mustapha Tinubu wanda ya bayyana cewa sunansa da ake laƙanawa da Tinubu a ciki ya…
Read More
Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Nijeriya

Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masana sun yi gargaɗin cewa matuƙar ba a magance matsalar tsaro ba, za a samu yawaitar ayyukan ta'addanci a nan gaba. Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Nijeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai…
Read More
Asalin bikin Mauludi da hawan Takutaha a Kano – Ra’ayoyin malamai da al’umma

Asalin bikin Mauludi da hawan Takutaha a Kano – Ra’ayoyin malamai da al’umma

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Bikin mauludi na takutaha ya jima ana gudanar da shi a Birnin Kano da jihar baki ɗaya, inda ake yin hawa da kuma shagulgula. Wannan ya sanya Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Kano ya bi sahun masu hawa Goron Dutse wajen bikin Hawan Takutaha, inda ya tattauna da malamai da mabiyan Mauludi kan muhimmancin wannan rana ta zagayowar haihuwar Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (SAW). Wannan al’ada ta shafe ɗaruruwan shekaru tana gudana daga ranar 12 ga Rabi’ul Awwal zuwa 19 ga watan, wacce a Kano aka fi sani da Takutaha. A wannan rana, jama’ar Kano,…
Read More
Shin akwai Sardauna a Arewa?

Shin akwai Sardauna a Arewa?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kowanne yanki ka iya samun wani jan gwarzo da kan sadaukar da kan sa don bunƙasa yankin. Akasarin irin waɗannan gwarazan ka iya tsintar kan su a gidan yari ko ma a yi mu su kisan gilla. Sauƙin lamarin shi ne aiyukan alherin irin wadannan mutane kan wanzu shekaru aru-aru bayan rayuwar su. Idan mutum ya shuka alheri to ba shakka alherin zai bi shi har ma ya iya amfanar zuriyar sa su zama masu albarka. Hausawa kan ce alheri gadon barci. Mu duba rayuwar Shehu Usmanu Mujaddadi wanda dududu shekara 63 ya yi a duniya…
Read More