30
Nov
Daga IBRAHUM MUHAMMAD a Kano Mai bai wa Shugaban ƙaramar Hukumar Dala shawara akan muhalli, Hajiya Ummi Alasan ƙofar Ruwa ta bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kano da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Shehu Wada Sagagi da 'yan majalisun Dala da Kwamishina Ibrahim Namadi da jagoran Kwankwasiyya na Dala ɗayyabu Ahmad Maiturare bisa goyon bayansu wajen ba ta muƙamin. Ta ce sun samu shugaban ƙaramar hukumar Dala Suraj Imam Mutum ne jajirtacce mai ilimi na zamani da na addini da yake yin ƙoƙarin haɗin kai a wannan tafiya da suke ta Kwankwasiyya amana. Hajiya Ummi Alasan Kofar Ruwa ta yi nuni…
