Labarai

Nijeriya ta tabbatar da mutum 67 sun kamu da ƙyandar biri a jihohi 23

Nijeriya ta tabbatar da mutum 67 sun kamu da ƙyandar biri a jihohi 23

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Nijeriya ta tabbatar da mutum 67 ne suka kamu da cutar ƙyandar biri daga cikin mutum 1,031 da aka yi fargabar sun kamu da cutar a jihohi 23, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta wallafa a ranar 11 ga Satumba. Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC ta ce jihar Akwa-Ibom da Enugu kowacce na da mutum takwas da suka kamu, sai Bayelsa da ke da shida, sai kuma Kuros Riba mai biyar, da kuma sauran mutum 40 ɗin da suka watsu a sauran jihohi…
Read More
‘Yan jihar Sakkwato da suka tsere wa ‘yan bindiga zuwa Nijar na cikin wani hali

‘Yan jihar Sakkwato da suka tsere wa ‘yan bindiga zuwa Nijar na cikin wani hali

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jamhuriyar Nijar wasu 'yan gudun hijira da suka tsere daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato sakamakon tashin hankalin 'yan bindiga wanda suka yada zango a garin Abalak a jihar Tahoua na cikin mawuyacin hali. 'Yan gudun hijirar da suka haɗa da mata da ƙananan yara, na rayuwa cikin wahala inda matan sai sun yi bara suke samun abin da za su ci, watarana kuma su kwana da yunwa. Kawo yanzu dai babu cikakkiyar ƙididdiga ta yawan mutanen da suka tsere daga yankunansu suka shiga Nijar sakamakon matsalar tsaron. Bayanai dai…
Read More
Jiragen soji sun kashe ’yan ta’adda 28 a Neja

Jiragen soji sun kashe ’yan ta’adda 28 a Neja

 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga aƙalla 28 ne jiragen sojin saman Nijeriya suka hallaka a yankin Bassa, ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta ce jiragen sun ragargaji ’yan ta’addan ne da haɗin gwiwar sojojin ƙasa. Mataimakin Darakta Yaɗa Labarai na Rundunar, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce a yayin aikin sharar ’yan fashin daji ne sojojin suka yi arba da gungun wasu ’yan ta’adda kimanin 100. Kyaftin Ali ya ce, “da samun rahoto ne jiragen suka je suka ragargaji ’yan ta’addan, inda aka gano gawarwakin 28 daga cikinsu. “A halin yanzu ana…
Read More
Tinubu ya gaza cika wa ‘yan Nijeriya alƙawarin da ya ɗauka – Lukman

Tinubu ya gaza cika wa ‘yan Nijeriya alƙawarin da ya ɗauka – Lukman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya yi iƙirarin cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaza cika alƙawarin da ya yi na samar da “sabon bege” ga ‘yan Nijeriya. Mista Lukman, wanda ya yi wannan iƙirarin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Tɓ’s Politics a ranar Laraba, ya koka da yadda abubuwa ke ƙara ta’azzara a ƙarƙashin shugaban ƙasa. A cewarsa, akwai ƙarin wuraren da ba gwamnati ba a ƙarƙashin kulawar gwamnati mai ci. Ya ce: “Idan muka zaɓi shugabanni, bisa alƙawuran da suka ɗauka, misali…
Read More

Yadda Isra’ila ke cigaba da cin karenta ba babbaka a yaƙinta da Palestine

Daga BELLO A. BABAJI Bayan shafe tsawon kwanaki 342 ƙasar Isra'ila na buɗe wuta wa makofciyarta ta Palastine, sojojin Isra'ila ƙarƙashin jagorancin shugabannin siyasa da na soji tare da taimakon Amurka, na cigaba da kisan kiyashi da rushe gine-gine da ɗaiɗaita al'ummar Palestine a wani yunƙuri na ramuwar gayya. Cikin wata takarda da Jakadan Palestine, Abdullah Abu Shawesh ya fitar, ya ce haɗin-gwiwa tsakanin Isra'ila da Amurka akan mutanen Palestine na ɗaya daga cikin mummunan yanayi da aka taɓa shiga a tarihi kamar yadda ƙididdiga ta nuna. Ya ce, ƙasashen da a duniya suke ikirarin sun fi kowa ƙoƙarin kare…
Read More

Tinubu ya gana da Sarki Charles na uku a Fadar Bakinham da ke birnin Landan

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga sarkin Ingila, Sarki Charles na uku a Fadar Bakinham da ke birnin Landan don gudanar da ganawa ta kai-da-kai a wani mataki da ke nuni da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da ƙasar Ingila. A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samo, wannan ita ce ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu tun bayan haɗuwarsu a wajen taron canjin yanayi karo na 28 da aka yi a bara a ƙasar Dubai. Ganawar ta yanzu ta biyo bayan amsa gayyatar da sarkin na Ingila ya yi ma sa. Shugabannin sun tattauna…
Read More

Gwamnan Zamfara ya raba magungunan sama da biliyan N1 da kayan agaji na gaggawa ga asibitoci a jihar

Daga BELLO A BABAJI Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin raba magunguna da kayayyakin kariya na kai-da-kai (PPE) da na bada agajin gaggawa ga asibitoci a jihar. A ranar Alhamis ne aka gudanar da haka a asibitin cutukan sanyi (IDH) a Damba da ke Gusau, babban birnin jihar. Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris acikin wata takarda da ya fitar, ya ce aikin na ɗaya daga cikin ababen da gwamnatin jihar ta shirya don inganta zamantakewar al'ummarta. Ya ce, magungunan sun kai na adadin sama da Naira biliyan ɗaya waɗanda aka raba wa ɓangaren harkar lafiya don bunƙasa shi.…
Read More

Mutane 15 sun mutu sakamakon ambaliya a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.Mamakon ruwan sama ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 a yayin da wasu 3,094 suka rasa muhallansu a wasu yankunan jihar Katsina. Hajiya Binta Husaini wacce ita ce shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, ta sanar da manema labarai a ofishinta. Ta ƙara da cewa, aƙalla mutane 21,481 ne suka samu raunuka a yayin aukuwar lamarin. Haka kuma, gidaje 32,542 suka rushe a ƙananan hukumomi 32 da ke faɗin jihar. Hajiya Binta ta bayyana ƙananan hukumomin Dutsinma, Daura, Kaita, Katsina da Batsari a matsayin waɗanda ambaliyar ta fi yi musu ɓarna. Haka nan, ambaliyar ta…
Read More

‘Yan sanda 32 ke tsaron ƙauyuka sama da 200 a Katsina – Raɗɗa

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana cewa rashin isassun jami'an tsaro da kayan aiki sun taka rawa wajen ta'azzar rashin tsoro da ake fama da shi a jihar. A tattaunawarsa da tashar DW, gwamna Raɗɗa ya ce akwai ƙaramar hukuma mai ƙauyuka sama da 200 a jihar wadda ƴan sanda 32 ne kawai ke samar da tsaro ga al'ummar yankunan. "A jihar Katsina akwai ƙaramar hukumar da ke da ƴan sanda 32. Bindigarsu guda tara ce, mai aiki kuma guda biyar ce, ƙaramar hukumar da ke da ƙauyuka kusan 200. Mazaɓu sama da goma. Ya za a yi…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyar da soja uku a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyar da soja uku a Zamfara

Daga USMAN KAROFI a Abuja Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar da sojoji uku a wani mummunan harin kwantan ɓauna da suka kai a safiyar ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. An kai harin ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke rakiyar ma’aikatan kamfanin gine-gine na Setraco Nigeria Limited. Wani majiyar soji ya tabbatar wa 'yan jarida wannan mummunan al’amari, inda ya bayyana cewa jami’an tsaron ba su yi ƙasa a gwiwa ba a lokacin da ‘yan ta’addan suka buɗe wuta. Wannan harin kwantan ɓaunan ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro takwas da…
Read More