Labarai

Jami’an tsaron al’umma sun kama mota ɗauke da albarusai 610 a Katsina

Jami’an tsaron al’umma sun kama mota ɗauke da albarusai 610 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'an tsaron al'umma(CWC) sun kama wata motar haya ɗauke da albarusai a tsakanin Katsina zuwa Batsari Babban jami'in tsaro da ke kula da ƙaramar hukumar Batsari Ahmed sunusi Batsari ya bayyana haka a Katsina lokacin da ya gabatar da albarusan gaban kwamishinan harkokin tsaro da harkokin cikin gida Dr Nasir mu'azu Danmusa. Yace motar da ke ɗauke da fasinja guda 17 jami'an sa sun tsaida sune akan hanyar Katsina zuwa Batsari. Babban jami'in tsaron ya ƙara da cewa a lokacin da suke gudanar da bincike sai ya lura da ɗaya daga cikin fasinja baya cikin…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar koma wa makarantu a jihar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Kano ta sanar da sabuwar ranar komawa makarantu domin cigaba da ɗaukar karatu a sabon zango na shekarar 2024/2025. Daraktan wayar da kan al'umma a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Ƙiru ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. Ya ce, ɗaliban da ke makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, su kuma ɗaliban jeka ka dawo za su koma ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024. Makarantun da za a koma karatun sun haɗa da firamare, ƙaramar sakandire da kuma babbar sakandire mallakar…
Read More
Ƙungiyar Hausawan Afirka ta karrama Jaridar Blueprint da wakilinta na Kano

Ƙungiyar Hausawan Afirka ta karrama Jaridar Blueprint da wakilinta na Kano

Daga AISHA ASAS Al'ummar Hausawan Afirka (AHAD) ta karrama Jaridar Blueprint da ke buga jaridun Turanci da ta Hausa Blueprint Manhaja da kuma Wakilinta na jihar Kano Ibrahim Hamisu, a ranar makon Hausa ta duniya da ake gabatarwa a duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara. A yayin da ya ke miƙa takardar ƙwarewar, Shugaban Al'ummar Hausawan Afirka Sardaunan Agadas AMB (Dr.) Abdulƙadir A. Koguna ya bayyana cewa, ganin irin gudunmuwar da Jaridar Blueprint ta ke bayarwa wajen bunƙasa da yaɗa harshen Hausa a Nijeriya. Ya ƙara da cewa Ibrahim Hamisu kuwa mutum ne jajirtaccen da a ko da…
Read More

An naɗa Sani Musa a matsayin Daraktan Labarai na Kwalejin Kiwon Lafiya ta Zaria

Daga BELLO A. BABAJI Tsangayar Labarai ta Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon da ke Zaria a jihar Kaduna ta samu sabon Darakta bayan da aka bai wa Sani Musa Daitu muƙamin. Cikin wani saƙo da ya fitar, Musa Daitu ya ce "ina farin cikin sanar da ku cewa, Ni, Sani Musa Daitu, an naɗa Ni a matsayin Daraktan Labarai a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Al-Haroon da ke Zaria." Ya ce, an ba shi muƙamin ne wanda zai riƙe na tsawon shekaru uku (2024-2027), ya na mai alƙawarin zai yi aiki tuƙuru wajen ganin an cimma manufofin ofishin. Ya ƙara da…
Read More

Gwamna Dauda ya bada biliyan N11 ga ilimin ƴaƴa mata a Zamfara

Daga BELLO A BABAJI Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ƙaddamar da aikin raba tallafi ga ƙananan makarantu (SIGS) a ƙarƙashin shirin inganta mata da ba su ilimi (AGILE) a jihar. A ranar Laraba ne gwamanan ya miƙa takardun bada ayyukan ga ƴan kwangilar gyarana makarantu. Cikin wata sanarwa da kakakin gwamanan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce an shirya aikin ne musamman don inganta hanyoyin samun karatu, cigaba da karatu da kuma biyan wani kaso a makarantun jihar. Ya kuma ce, wannan shi ne zangon farko na shirin SIGS ƙarƙashin ayyukan AGILE. A lokacin da ya ke…
Read More

Ambaliya: Shettima ya tallafa da tirela 50 na shinkafa ga ƴan Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ziyarci Maiduguri don jajenta wa al'ummar Borno kan ambaliyar tafkin Alau da ta ɗaiɗaita dubunnan mutane. Shettima, wanda ya jagoranci tawagar Fadar gwamnatin tarayya, ya samu tarba daga gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum inda ya kai shi Fadar Shehun Borno wanda nan ma ambaliyar ta shafa. Daga nan ne Mataimakin shugaban ƙasar ya garzaya zuwa sansanin Bakassi inda aka kai waɗanda suka rasa matsugunansu. Ya bayyana musu cewa, gwamnatin tarayya za ta tallafa musu da tirela 50 na shinkafa. Ya ƙara da cewa, gwamnati tare da…
Read More

Ambaliya: Za a samu ɓarkewar kwalara, rashin abinci da tsaro a Maiduguri – Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da yiyuwar ɓarkewar cutar kwalara a sansanonin ƴan gudun hijira na wucin-gadi da aka kafa a Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye jihar. Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya fitar, yace abubawan da za’a buƙata cikin gaggawa sun haɗa da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa, inda ya ƙara da cewar wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurɓace kuma na iya janyo ɓarkewar cututtuka irinsu kwalara. An ruwaito rahoton na cewa, “buƙatun gaggawa da ake dasu sun…
Read More

Ajaero bai fi ƙarfin doka ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Offishin shugaban ƙasa ya kare maganar kama shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) Joe Ajaero inda ya ce bai fi ƙarfin dokar ƙasa ba. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. A ranar Litinin ne jami'an DSS suka kama Ajaero a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a lokacin da ya nufi Burtaniya wanda sai bayan sa'o'i 15 ne suka sako shi. Hakan ya haifar da cecekuce acikin al'ummar ciki da wajen Nijeriya da…
Read More
BIDIYO: Yadda asibitin Best Choice ya ƙaddamar da sabuwar na’urar jarirai ta ‘Jaundice’ ta farko a Arewa

BIDIYO: Yadda asibitin Best Choice ya ƙaddamar da sabuwar na’urar jarirai ta ‘Jaundice’ ta farko a Arewa

Daga NASIR S. GWANGWAZO "Hanyar Cigaban Arewacin Najeriya!" A wani yunƙuri na inganta kula da kiwon lafiya, asibitin ƙwararru na Best Choice ya ɗauki gabaren kula da kiwon lafiyar jarirai tare da ƙaddamar da Sashin fasaha don kula da Lafiyar Jarirai da aka tsara don magance ciwon shawara da hana lalacewar kwakwalwar ga jarirai. A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban asibitin, Auwal Muhammad Lawal, ya lura cewa na’urar ita ce irinta ta farko, wanda ƙwararrun likitoci ke amfani da ita wajen juyen jini cikin fasaha don inganta sakamakon jiyya ga yara. A nan ɓangaren Dr Abdulmalik…
Read More

Nan ba da jimawa ba za mu kamo Bello Turji – Janar Musa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Ma'aikatan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa ya tabbatar wa al'ummar Nijeriya cewa nan ba da jimawa ba za su kama shahararre kuma shugaban ƴan ta'addar nan, Bello Turji. Janar Musa, ya faɗi haka ne a ranar Talata, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja yayin bada bayanai game da ayyukan jami'an tsaro a Nijeriya. Ya ce, "kama Turji na daf da faruwa", inda ya bayyana ɗan ta'addan a matsayin wanda ke jin ya bunƙasa, ya na mai cewa hakan na wani ɗan lokacin ne yayin da jami'an sojoji ke cigaba da…
Read More