17
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministan Labarai da Haɗin kan Ƙasa, Mohammed Idris ya yi kira ga ƙungiyoyin gidajen jaridu na ƙasa-da-ƙasa su ke yin adalci wajen ruwaito labaran da su ka shafi Nijeriya a kowane matakin na harkar jarida. Idris ya yi kiran ne a lokacin da Mataimakin shugaban gidan BBC, Johnathan Munro da tawagarsa suka ziyarce shi ranar Alhamis a Abuja. Ya ce, tsarin gudanarwa ta gwamnatin Shugaba Tinubu a ɓangaren harkar yaɗa labarai ta na nan wajen bai wa al'umma yancinsu na watsa labarai tare samar da cigaba a gare su. Ya ƙara da cewa, gidajen jaridu na…
