Labarai

OCSC ta buƙaci Tinubu ya mayar da tallafi man fetur

OCSC ta buƙaci Tinubu ya mayar da tallafi man fetur

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na fuskantar matsin lamba na maido da tallafin wutar lantarki da man fetur, yayin da ƙungiyoyin farar hula a jihar Osun suka yi gargaɗin yiwuwar sake ɓarkewa da zanga-zanga matuƙar ba a biya musu buƙatunsu ba. Gamayyar ƙungiyoyin farar hula na jihar Osun (OCSC) da ke wakiltar aungiyoyin fararen hula daban-daban a jihar, sun fitar da sanarwa a ƙarshen zanga-zangar ta #EndBadGovernance na kwanaki 10, inda ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa. Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban OCSC Waheed Lawal, ta soki jawabin da Shugaba Tinubu…
Read More
Na sa hannu kan yarjejeniya da ‘yan China ne bisa kuskure – Amosun

Na sa hannu kan yarjejeniya da ‘yan China ne bisa kuskure – Amosun

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya bayyana cewa an yaudare shi wajen bayar da mallakin fagen kasuwanci ga mayaudaran 'yan China masu zuba hannun jari. Amosu wanda ya kasance gwamnan Ogun daga 2011 zuwa 2019, ya fitar da wata sanarwa inda ya ke bayyana cewa tabbas bai yi zurfin bincike ba wajen miƙawa kamfanin 'yan China mallakin "Ogun-Guadong Free Trade Zone" waɗanda yanzu ke neman kwace kadarorin gwamnatin Nijeriya a ƙasashen yamma da Amurka. Amosun ya ƙara da cewa, "Ogun Free Trade Zone" gwamnatin bayan shi ce ta fara assasa wannan aiki inda shi ma ya gada. Bayan hawan…
Read More
 Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin ɗaure waɗanda suka ƙi rera sabon taken Nijeriya

 Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin ɗaure waɗanda suka ƙi rera sabon taken Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Wakilan Nijeriya ta bayyana cewa an janye ƙudurin dokar da za ta hukunta ’yan Nijeriya da suka ƙi rera sabon taken ƙasa. Daga cikin tanade-tanaden ƙudirin, akwai hukunta masu wulaƙanta alamomin ƙasar nan da kuma lalata wurin ibada a faɗin Nijeriya. Majalisar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa shugaban majalisar da kansa ne ya bijiro da ƙudurin a ranar Talata , 23 Yuli, 2024, kuma tuni ya jawo Allah-wadai daga jama'ar ƙasa. Majalisar ta ce, shugabanta ya zurfafa bincike domin gano ko ƙudurin zai yi daidai da cigaban 'yan ƙasar nan domin tabbatar da…
Read More
EFCC ta bayar da gudunmawar biliyan N50 daga kuɗaɗen da ta ƙwato don tallafa wa ɗalibai

EFCC ta bayar da gudunmawar biliyan N50 daga kuɗaɗen da ta ƙwato don tallafa wa ɗalibai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Masi Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayar da gudunmawar zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 50bn domin tallafa wa Asusun Lamunin ɗalibai na Nijeriya (NELFUND). Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024, lokacin da Manajan Daraktan Asusun kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Akintunde Sawyerr, ya jagoranci tawagar gudanarwar zuwa ziyarar ban girma a hedikwatar EFCC da ke Abuja. Sawyerr ya bayyana cewa, asusun, wani shiri na gwamnatin shugaba Bola Tinubu, an tsara shi ne don samar da kuɗaɗe don ilmantar da ɗalibai marasa galihu. Sanarwar da…
Read More

Gwamnan Zamfara ya jajenta wa waɗanda ambaliya ta rutsa da su a Gummi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajenta wa mutanen da haɗarin ambaliyar ruwan sama ya rutsa da su a ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar. A ranar Juma'a ne wani mamakon ruwan sama da aka yi a wasu yankunan ƙaramar hukumar ya ɓarnata gidaje da dama. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce gwamnan ya nuna damuwar matuƙa tare da tausayawa waɗanda al'amarin ya shafa inda ya ce ya na tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki tun bayan aukuwar lamarin da suka haɗa da; hukumomi, shugabannin da masu faɗa a ji a…
Read More

Hukumar Kwastom ta yi ƙarin haske kan harajin shigo da shinkafa ta iyakar ƙasa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar Kwastom, NCS ta ce umarnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na shigo da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba bai kunshi shigo da hatsi ba ta kan iyakokin ƙasa a Nijeriya. A shekarar da ta gabata ne gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur wanda hakan ya yi sanadiyyar tashin gwaoron zabi ga farashin kayan abinci da kuma karya darajar Naira wadda kasuwanci duniya ke sarrafata. Hakan ya shafi shinkafa wadda ta na ɗaya daga cikin abincin da mafi yawancin ƴan Nijeriya ke amfani da shi inda a…
Read More

Tinubu da Shettima sun karɓi baƙoncin tawagar matasa a taron ilimintarwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A wani yunƙuri na inganta matasa a Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima da Shugaban Jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje sun shirya jagorantar taron ilimintarwa na matasa a ranakun 3 zuwa 5 ga watan Satumban 2024 a Fadar shugaban ƙasa. An shirya taron ne ta ofishin shugaban matasan jam'iyyar APC na Ƙasa domin ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da matasan da kuma shiga cikin harkar tsare-tsaren shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da cigaba mai ɗorewa a Nijeriya. Cikin ababen da taron ya ƙunsa akwai fage na tattaunawa tsakanin gwamnati da matasan inda za a…
Read More

Lokacin satar ɗanyen mai ya zo ƙarshe a Najeriya – Doguwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamitin musamman kan satar ɗanyen mai na Majalisar Wakilai ya gargaɗi al'umma da babbar murya cewa ayyukan satar ɗanyen mai ya zo ƙarshe a ƙasar tare da alwashin duk wanda aka kama da hannu akan haka, to zai fuskanci hukuncin doka. Shugaban kwamitin, Alhasan Ado Doguwa ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a ranar Juma'a. Ya ce, ba za su bari gwamnatin shugaba Tinubu/APC ta cigaba da ciyo bashi daga ƙasashen waje ba sakamakon giɓi da ake samu a ɓangaren harkar mai da gas a Najeriya. Ya kuma ce, ana samun…
Read More

Shugaba Tinubu ya taya Janar Babangida murnar cika shekaru 83

Daga NASIR S. GWANGWAZO Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya miƙa sakon taya murna ga tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida wanda ke cika shekaru 83 a duniya a yau, 17 ga watan Agusta. A cikin wata sanarwa da ta fito daga Fadar gwamnatin tarayya, shugaba Tinubu ya yaba wa irin gudunmawar da Janar Babangida ya bayar wajen ci gaban Nijeriya, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, inda ya bayyana kammala aikin gadar nan ta Third Mainland Bridge wadda ita ce gada mafi tsawo a Afirka a lokacin a matsayin aikin da ba za a manta…
Read More

Sojoji sun kashe ƴan bindiga biyu a Zamfara

Daga Sanusi Muhammad a Gusau Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta 1 Brigade da Sector 1 Joint Task Force (North West) Operation Hadarin Daji (OPHD) a ƙarƙashin 'Operation Sahel Sanity II', sun yi nasarar kashe ƴan bindiga biyu a ƙoƙarin da sojojin ke yi na samun nasarori a yaƙin da su ke yi da ƴan bindiga a jihar Zamfara. Daraktan hulɗa da jama'a na1 Brigade/Sector 1 OPHD, Lt Suleiman Omale ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa Blueprint ranar Asabar. "A ranar 16 ga watan Agustan 2024, sojojin bisa umarnin kwamandan runduna ta 1 na sojojin Najeriya da…
Read More