Labarai

Gidaje fiye da 250 ne suka ruguje sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina

Gidaje fiye da 250 ne suka ruguje sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya kawo rugujewar gidaje fiye da 250 a garin Natsinta da ke karamar hukumar Jibiya a Jihar Katsina. Ruwan saman da ya ɗauki kusan kwanaki uku ana zabgawa a jihar ya kawo sanadiyyar faɗuwar gidaje ba a garin Natsinta ba ka ɗai harda wasu sassan jihar. Ɗan majalisar dokokin mai wakilta karamar hukumar Jibiya Mustafa Yusuf ya nuna alhinin sa da jajantawa mutanen da suka rasa gidajen su. Ɗan majalisar wanda ya ke magana a sa'ilin da ya kai ziyarar janjantawa ga al'ummar garin ya tabbatar masu da cewa…
Read More

LP, YPP da AAC sun lashe kujerun kansiloli a Bauchi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Jam'iyyun adawa a jihar Bauchi sun lashe da dama daga cikin kujerun kansiloli a zaɓen da aka yi a ranar Asabar. A jihar, wacce jam'iyyar PDP ke mulki ƙarƙashin jagorancin gwamna Bala Mohammed, aka samu Samira Maikano ta lashe kujerar gundumar Wandi da ke ƙaramar hukumar Dass a jam'iyyar YPP. Samira ta samu ƙuri'u 1,610 wanda hakan ya ba ta galaba akan abokin hamayyarta na kusa Bashir Abdullahi na jam'iyyar PDP da ya samu ƙuri'u 1,352 yayin da APC ta samu kuri'u 230. A ƙaramar hukumar Darazo, Yunusa Muhammad na jam'iyyar AAC shi ya lashe zaɓen…
Read More

‘Yan sanda da ƴan banga sun ceto matafiya 20 bayan garkuwa da aka yi da su a Kwara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar ƴan sanda a jihar Kwara ta ce ta yi nasarar ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a hanyar Osi/Obbo Aiyegunle da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar. Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce tawagar rundunar tare da haɗin gwiwar ƴan bijilante da aka fi sani da ƴan banga suka gudanar da atsayen. Ta ce, jami'an sun ceto baki ɗaya mutanen a raye yayin da aka garzaya da wasu mutum uku da ke ɗauke da raunuka asibiti domin ba su kula. Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen da aka yi…
Read More

Mahaifiya da ƴaƴanta biyar sun mutu bayan cin gurɓataccen ɗan-wake a Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu mutane shida a ƙauyen Karikari da ke ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano sun rasa rayukansu sakamakon cin ɗan wake. Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis a gidan wani marigayi mai suna Malam Abdulkarim. Wani maƙofcin gidan, Garba Muhammad ya bayyana wa manema labarai cewa saboda tsananin rayuwa da yunwa, matar wacce ke ƙoƙarin ciyar da iyalanta ta yi amfani da gurɓataccen garin alabo wajen yi mu su girki. Ya ce, "cin abincin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida cikin ahalin, har da mahaifiyar." Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP…
Read More

Yadda aka matsa mana kan mu soke zaɓen shugaban ƙasa na 2023 – AbdulSalami

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamitin zaman lafiya na ƙasa, NPC ya bankaɗo wata maƙarƙashiya da aka samu daga ƴan jam'iyyu a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ganin yadda aka matsa masa kan sai dai ya tunzura hukumar zaɓen ta ƙasa (INEC) ta datakar ko kuma soke zaɓen. Kwamitin, wanda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar AbdulSalami Abubakar ke jagoranta, ya faɗi haka ne a ranar Juma'a a Abuja, a lokacin da ya gabatar da rahotonsa mai ɗauke da shafuka 106 na zaɓen 2023 mai suna; "Nigeria's Pursuit of Electoral Compliance: National Peace Committee NPC 2023 General Elections…
Read More

Tinubu ya umarci a rage adadin wakilan Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin duniya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A wani yunƙuri na rage adadin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a rage adadin wakilai da Nijeriya ta saba turawa zuwa taron majalisar ɗinkin duniya karo na 79 da za a yi a birnin New York da ke Amurka a watan Satumba. Sanarwar ta fito ne daga ofishin shugaban ma'aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila a ranar Asabar a wani taron kwana ɗaya da hukumar gudanarwa ta offishin ta yi. Hakan na zuwa ne bayan da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar…
Read More
A fim ɗin ‘Faliha and Falisha’ aka ba ni matsayin da babu wani furodusa a Kannywood da ya taɓa ba ni – Isa Ballo Ja

A fim ɗin ‘Faliha and Falisha’ aka ba ni matsayin da babu wani furodusa a Kannywood da ya taɓa ba ni – Isa Ballo Ja

DAGA MUKHTAR YAKUBU A satin da ya gabata ne aka kammala ɗaukar sabon shirin fim ɗin 'Faliha and Falisha' wanda kamfanin shirya finafinai na Today's Life Nigeria Limited na jaruma Mansurah Isah suka ɗauki nauyin shiryawa. Fim ɗin wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan finafinai da ita Mansurah Isah ta ɗauki nauyin shiryawa. An shafe kusan sati biiyu ana aikin tare da manyan jaruman Kannywood da suka haɗa da Mommy Gombe, Isa Ballo Ja, Timmah Makamashi da dai sauransu. Matashin mai bayar da umarni Darakta Isah Alolo shi ne ya bada umarni yayin da ita kuma Mansurah Isah ta…
Read More
Ƙungiyar Mahauta a Legas ta koka da yawan haraji

Ƙungiyar Mahauta a Legas ta koka da yawan haraji

Daga  ABDULLAHI AHMED a Legas Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Mahauta ta ƙasa,  reshan Jihar Legas ta koka da yadda gwamnati ta saka mata haraji mai yawa. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Ahmed ne ya bayyana haka ofishin ƙungiyar jim kaɗan bayan kammala taron su da waɗansu ƙusoshin ƙungiyar wanda suka saba yi a duk ƙarshen mako. Ya ce, shi da sauran mahauta masu gudanar da harkokin sana'arsu ta fawa a Legas suna cigaba da kokawa bisa ga yawan biyan kuɗaɗen harajin dabbobin da suke yankawa a mayankar shanun ta abbatuwa da ke Agege.  Kuma ya shaida wa Jaridar Blueprint Manhaja a Legas gaskiyar…
Read More
PDP ta zaɓi Abdullahi Tumburkai a matsayin Shugaban ƙungiyar ’Yan Takarar ƙananan Hukumomi a Katsina

PDP ta zaɓi Abdullahi Tumburkai a matsayin Shugaban ƙungiyar ’Yan Takarar ƙananan Hukumomi a Katsina

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jami'iyar PDP a Jihar Katsina ta zaɓi Honorabul Abdullahi Usman Tumburkai, ƙwararren ɗan jarida daga ƙaramar Hukumar Dandume a matsayin Shugaban ƙungiyar ’Yan Takarar jam’iyyar na zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar. An gudanar da zaɓen ne a Sakatariyar jam’iyyar da ke Katsina, inda zaɓaɓɓun ’yan takarar jam’iyyar 34 suka hallara a ranar Lahadin da ta gabata. Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na sa, Honorabul Hamisu Ismail Jibia. Sanarwar ta ce, "wannan matsayi yana nuna ƙudirin Abdullahi na samar da haɗin kai…
Read More