Labarai

Gwamnatin Tinubu ta biya albashin wata 45 da ake bi lokacin Buhari

Gwamnatin Tinubu ta biya albashin wata 45 da ake bi lokacin Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ƙarshe dai gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta biya mafi ƙarancin albashi na watanni 45 da Ma’aikatan Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NiMet ke bin gwamnatin da ta shuɗe. An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Agusta, 2024, mai ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin haɗin gwiwa na NiMet, Okechukwu Nwokoro, a ranar Litinin. Bashin da ba a biya ba, wanda ya samo asali tun daga shekarar 2019 - a lokacin gwamnatin tsohon shugaban aasa Muhammadu Buhari - ya kasance tushen tashin hankali tsakanin hukumar…
Read More
Gwamnatin Kano ta gurfanar da ‘yan kasuwa kan ƙarin kuɗin burodi

Gwamnatin Kano ta gurfanar da ‘yan kasuwa kan ƙarin kuɗin burodi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Sauraron ƙorafe-ƙorafen Al’umma da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta sanar a ranar Juma’a cewa ta samu umarnin kotu na gurfanar da wasu mutum bakwai da ake zargi da ƙara farashin kayayyaki na wuce kima, musamman fulawa, lamarin da ya haifar da ƙarin farashin burodi a faɗin jihar. A yayin wani taro da wakilan kasuwar hada-hadar kayayyaki da aka fi sani da Kasuwar Singer, da kuma ƙungiyar masu yin burodi, Shugaban Kamfanin PCACC, Barista Muhyi Rimingado, ya bayyana cewa dillalan da aka gano sune ke da alhakin tashin farashin na…
Read More
Yadda kurma ta lashe gasar sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu

Yadda kurma ta lashe gasar sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu

Mia le Rouɗ, ta zamo kurma sarauniyar kyau ta farko da ta lashe gasar kyau da aka yi a Afirka ta Kudu bayan takaddamar da aka samu a batun zaɓen wadda tafi kyau, inda ɗaya daga cikin masu fafatawar a gasar ta janye saboda zarginta da kasacewa ’yar Nijeriya. A jawabinta na godiya bayan sanar da wadda ta yi nasara,Ms Le Rouɗ, ta ce tana fatan nasararta za ta ƙarfafa gwiwar waɗanda ke ganin ana ware su a cikin al'umma. Ta ce tana so ta taimakawa waɗanda ba su da arfi da kuma waɗanda ke ganin ba su da damar…
Read More
Ya saki matarsa kan hirar waya da makwabcinsa

Ya saki matarsa kan hirar waya da makwabcinsa

Wani magidanci ya buƙaci kotu ta raba aurensa da matarsa bisa zarginta da cin amanar aure da yin hira da makwabcinsa ta shafukan sada zumunta. Da ya ke jawabi a gaban kotun, magidancin ya zargi matarsa cewa sau uku tana tafiya ta bar gidansa, ciki har da wani lokaci da ta bar gidan nasa na tsawon wata biyu. Ya kuma zarge ta da alaƙa da wani makwabcinsa wanda ta ke ɗaukar tsawon lokaci tana hira da shi ta intanet. Ya ce, “lokacin ƙarshe da ta bar gidan sai da ta daɗe kafin ta dawo, da ta dawo kuma sai ta…
Read More
Uba ya bindige jaririyarsa saboda ba ya son ’ya mace

Uba ya bindige jaririyarsa saboda ba ya son ’ya mace

Rundunar ’yan sanda a ƙasar Pakistan sun bazama wajen neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi ya kashe ’yarsa ’yar kimanin kwanaki bakwai da haihuwa. Ana zargin mutumin da harbe jaririyar ne saboda ba ya son ya fara haihuwar ’ya mace sai dai namiji. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne a birnin Mianwali da ke tsakiyar Pakistan. Bincike ya nuna cewa, jaririyar ta mutu ne nan take bayan harbinta sau biyar da bindiga da mahaifin ya yi. Kisan ya fusata jama’a tun bayan da aka sanya hoton gawar jaririyar a shafukan sada zumunta. ƙungiyoyin kare haƙƙin…
Read More
Sarkin Dutse, Marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi

Sarkin Dutse, Marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Marigari Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, CFR. Mutum ne mai ilimin addini da na zamani, ɗankasuwa, kuma mai son kyautatawa jama'arsa. Yana da jajircewa wajen ganin an aikata gaskiya a dukkan hali. Mutum ne mai son tafiye-tafiye. Rubutun da mai karatu zai karanta dangane da rayuwar Mai Martaba Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, an tsakuro shi ne daga littafin da shi Mai Martaba Sarki ya rubuta da hannunsa mai suna ‘The Days in My Life’. An haife ni da safiyar ranar Juma'a 5 ga watan Janairu na shekarar 1945 wanda ya yi daidai da…
Read More
LAFIYA UWAR JIKI: Olsa (gyambon ciki)

LAFIYA UWAR JIKI: Olsa (gyambon ciki)

Gabatarwa  Wannan ciwo na olsa, wato gyambon ciki, ciwo ne da yake ci wa al’umma da yawa tuwo a ƙwarya. Haƙiƙa mutane da yawa na fama da olsa. Babu ranar da za ka je asibiti ɓangaren “gastro” ba ka samu wanda ya zo da ƙorafin olsa ba.  Mutan gari (laymen) a gurinsu in an ce olsa, to ciki ta ke kamawa. Amma a matsayina na  malamin lafiya, na san akwai olsa iri daban daban da ke kama sassa na jikin ɗan adam. Ba zan kaiku nan ba, zan tsaya a iya olsar da ke kama kayan ciki kaɗai.  Da ina…
Read More
Gwamnan Kano ya bada umarnin yin bincike kan zargin kwangilar magunguna

Gwamnan Kano ya bada umarnin yin bincike kan zargin kwangilar magunguna

Daga USMAN KAROFI NASIR a Abuja Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin yin binciken a kan batun zargin bada kwangilar magunguna ga ƙananan hukumomi 44 da ke jihar. Gwamnan ya nuna rashin sani a kan wannan al'amari don haka ya umarci shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, Barr Muhuyi Magaji ya gudanar da binciken gaggawa a kan lamarin. Hakan ya fito ne a wata sanarwa da kwamishinan labarai Baba Halilu Ɗantiye da kuma mai ba gwamnan shwara a harkokin labarai Sanusi Bature Dawakin Tofa su ka sanyawa hannu, ta na cewa an umarci hukumar…
Read More
Gwamna Dikko Raɗɗa ya kai ziyara ƙasar Sin domin nemo masu zuba jari

Gwamna Dikko Raɗɗa ya kai ziyara ƙasar Sin domin nemo masu zuba jari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Yanzu haka gwamnan Jihar Katsina ya sauka a Beijing ƙasar Sin shi da tawagar sa a ƙoƙarin sa na nemo masu zuba jari a jihar. Wannan shine kama aiki na farko da yayi bayan kammala hutun wata ɗaya da yayi a ƙasashen waje. Ana sa ran wannan ziyara da ya kai za ta taimaka wajen samo masu zuba jari a jihar wajan fannin samar da cibiyar ƙera na'urorin bada hasken wutan lantarki mai amfani da hasken rana. Gwamna da tawagar sa za su kai ziyara a kamfanin Sinotruck da zai ɗauki har tsawon kwana biyar…
Read More

Ƴan bindiga sun kashe na hannun daman gwamnan Katsina da matarsa a ƙauyensu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta tabbatar da rahoton kisan Sanunsi Gyaza, wani na hannun daman gwamna Dikko Raɗɗa na jihar. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Abubakar Sadiq ya bayyana wa manema labarai ta wayar tarho a ranar Lahadi inda ya ce su na sane da al'amarin kuma suna gudanar da bincike a kai. Lamarin ya auku ne a ranar Juma'a da dare inda rahotanni suka bayyana cewa, ƴan bindigar sun kashe Sanusi ne a gidansa da ke Gyaza a ƙaramar hukumar Kankia wanda a sanadiyyar haka, matarsa ta farko ita ma ta…
Read More